Shugabannin Igbo sun nemi a hukunta wadanda suka sace yara 9 a Kano

Shugabannin Igbo sun nemi a hukunta wadanda suka sace yara 9 a Kano

Rahotanni sun kawo cewa wasu shugabannin kabilar Igbo sun jaddada cewa ya zama dole a zartar da hukunci akan wadanda suke yi safarar yara tara daga jihar Kano zuwa yankin Kudu.

A makon da ya gabata ne rundunan yan sanda reshen Kano ta bada sanarwa na cewa ta kama masu laifi takwas wadanda suka shahara a siya da siyar da yara da kuma safarar kananan yara.

Rundunar yan sandan tace ta bi duddugen mambobin kungiyar ne zuwa Onitsha a jihar Anambra, an kuma ceto yara tara.

A wani jawabi a ranar Laraba, Ebenezer Chima, shugaban kungiyar kabilar Igbo a Kano da Boniface Ibekwe, Sarkin Ndigbo sun yi Allah wadai da abunda masu laifin suka aikata.

Sun yi kira ga hukumar yan sanda da ta zartar da hukunci akan su kamar yanda doka ta tanadar.

Sun yabi gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje da Muhammadu Sanusi, Sarkin Kano bisa yanda suka dauki mataki a kan lamarin.

Shugabannin kabilar na Igbo har ila yau sun yabi jami’an tsaro bisa “yanayin yanda suka gudanar da bincike da hadin gwiwar da yayi sanadiyyar ceto yaran”.

KU KARANTA KUMA: Shugaba Buhari ya yi martani akan gobarar Onitsha

A ranar Litinin ne dai kungiyar kare hakkin Musulmi (MURIC) tayi kira ga a kwantar hankali a kan lamarin.

A wani jawabin da darektan kungiyar, Ishaq Akintola ya gabatar, kungiyar ta bukaci kiristoci dasu bayyana duk wasu bata gari dake cikinsu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel