Wata jami’a ta kori malami tare da janye shaidar digirin digirgir dinsa

Wata jami’a ta kori malami tare da janye shaidar digirin digirgir dinsa

Biyo bayan binciken da jaridar Punch tayi, ta bankado asirin wani malamin jami’ar Nnamdi Azikiwe da ke Awka. Hakan kuwa yasa jami’ar suka koresqa tare da kwace digirinsa na digirgir da yayi a jami’ar. A halin yanzu hukumar jami’ar na zargin kwalin digirinsa na biyu shima na bogi ne.

Jami’ar Nnamdi Azikiwe ta dauki Peter Ekemezie aiki ne a watan Yuli na shekarar 2010. Amma daukarsa aikin ya jawo hargitsi kala-kala saboda an daukesa ne a matsayin malamin jami’a mai matsayin farko a maimakon mai matsayi na biyu.

A 2013, wata mata mai suna Egolum ta yi ikirarin cewa wanda ake zargin ya karbi hanci hannun ta akan cewa zai samar mata da gurbin karatu a jami’ar Fatakwal.

KU KARANTA: Ko sau nawa zamu tsaya gaban alkali, mu ke da nasara, in ji ‘yan shi’a

Bayan bincike daga kwamiti na musamman da jami’ar ta wakilta, an bankado cewa Ekemezie na amfani da kwalin digirin farko na bogi ne daga jami’ar Fatakwal. Binciken da jami’ar ta ki amfani dashi wajen ladaftar da malamin.

Shekaru kadan bayan nan, wasu malaman jami’ar sun zargi Ekemezie da satar basirarsu don samun karin girma, zargin da wani kwamitin makarantar ya tabbatar. Kamar na digirin bogin, shima ba a dau wani mataki ba.

Ekemezie ya harbi kansa a kafa inda ya mika korafi ga kwamishinan jihar akan wasu abokan aikinsa na bakin cikin karin girmansa. A wannan binciken an sake gano takardar digirinsa ta farko ta bogi ce.

Daga nan ne wakilin Punch ya fara bincike akansa.

A binciken ne aka bankado cewa, digirin digirgir dinsa ma a watanni 14 ya kamalla; abinda ke daukar karancin watanni 36. Bayan nan ne jami’ar ta dakatar dashi a watan Yuli inda ta umarci malamanta da su kawo takardunsu don sabon tantancewa.

Bayan haka ne hukumar makarantar ta musanta samun kwalin digiri na biyu daga gareta tare da kwace digirin digirgir dinsa. Hakan kuwa ya jawo korarsa daga aiki tare da sanar da jama’a don su sahida.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel