‘Yan daba sun sake yin awon gaba da wani malamin makaranta a Kaduna

‘Yan daba sun sake yin awon gaba da wani malamin makaranta a Kaduna

Wadansu ‘yan daba dauke da bindigogi sun yi gaba da shugaban makarantar firamaren Danmagaji, Abdulhafiz Abdullahi tare da wasu mutum biyu a wani gidan mai dake Doka.

Shugaban jami’an tsaron Vanguard na Birnin-Gwari, Ibrahim Nagwari ya sanar damu cewa ‘yan bindigan sun raunata wadansu mutane biyu a sakamakon harbi da bindiga.

KU KARANTA:Aisha Buhari za ta ginawa Kungiyar AFLPM katafaren ofis a Abuja

Idan baku manta ba a ranar 2 ga watan Oktoba, wadansu ‘yan bindiga suka sace malamai biyu da dalibai shida a makarantar Engraver’s College dake kauyen Kakau Daji a karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna.

Bayan mako guda da sace dalibai shida da malamai biyu na kwalejin Engraver’s an sake dauke wasu dalibai shida a makarantar jeka ka dawo ta gwamnati dake Gwagwada a karamar hukumar Chikun a lokacin da suke hanyar tafiya makaranta.

Kauyukan dake makwabtaka da Birnin-Gwari sun dade suna fama da matsalar ‘yan bindigan tun lokacin da abin ya fara har zuwa yau.

Kamar yadda Nagwari ya bada labari ga jaridar Daily Nigerian ya ce: “ A safiyar Laraba da misalin karfe 8:30 ne wadansu ‘yan bindiga suka bude wuta ga matafiya hanyar Polwaya inda suka sace wani mai sayar da biredi a bakin hanyar.

“Duk a ranar Laraban ‘yan bindigan sun sake sace wadansu mutane da bamu san adadinsu ba a kauyen Gayam. A cikin makonni uku da suka wuce ta’addancin ‘yan bindiga ya dawo yankinmu na Birnin-Gwari.

“Kullum sai ‘yan bindiga sun fito bisa hanyar Birnin-Gwari zuwa Kaduna domin yin aiki, inda kuma suke cin karensu ba babbaka ba tare da jami’an tsaro sun kawo mana dauki ba.” Inji Nagwari.

https://dailynigerian.com/just-in-another-teacher-abducted-in-kaduna/

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel