Shugaba Buhari ya yi martani akan gobarar Onitsha

Shugaba Buhari ya yi martani akan gobarar Onitsha

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Alhamis, 17 ga watan Oktoba ya nuna alhini akan fashewar tankar mai a Onitsha wanda yayi sanadiyar rasa ran wasu mutane, tare da asarar dukiya.

A wani rubutu da shugaban kasar ya wallafa a shafinsa na twitter ya mika ta’aziyya ga wadanda suka rasa masoyansu, inda ya nuna tausayawa ga gawar wata uwa da danta wadanda annobar ya cika da su.

Haka zalika Buhari ya yi jaje ga wadanda suka rasa shaguna, gidaje da dukiyoyinsu a lamarin.

Buhari ya kuma yi kira ga daukar matakin gaggawa akan yawan afkuwar irin wannan annobar a hanyoyin jama’a, inda ya kara da cewa ya zama dole a tursasa mammalakan ababen hawa bin dokoki da suka yi watsi da shi.

Ga yadda ya wallafa a shafin nasa: "Lamarin gobarar da ya afku a Onitsha a jiya abun bakin ciki ne da kuma danasani. Gawar wata uwa da danta da wannan abun bakin cikin ya cika da su, da na gani ya taba zuciyana sosai.

KU KARANTA KUMA: Duniya ina za ki da mu: An tsinci jariri sabon haihuwa da ransa zindir a wani dajin Kaduna

"Ina mika jajena ga dukkanin wadanda wannan lamari ya cika dasu, wadanda suka rasa gidaje, shaguna da sauran kayayyakinsu.

"Ina kira ga daukar matakin gaggawa game da yawan faruwar wannan annobar a hanyoyin jama’a. Ya zama dole a tursasa bin doka da mammalakan ababen hawa suka wancakalar."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel