Duniya ina za ki da mu: An tsinci jariri sabon haihuwa da ransa zindir a wani dajin Kaduna

Duniya ina za ki da mu: An tsinci jariri sabon haihuwa da ransa zindir a wani dajin Kaduna

- Jami'an NSCDC a jihar Kaduna na cigaba da nemana bayanai game da wani jinjiri sabon haihuwa da aka tsinta da ransa

- Wata mata ce ta tsinci jinjirin ne zigidir ba kaya a cikin wani daji da ke yankin karamar hukumar Jema'a

- A yanzu haka jinjirin na cikin kosin lafiya a cibiyar Salama

Hukumar tsaro na NSCDC a karamar hukumar Jema’a na jihar Kaduna na cigaba da nemana bayanai game da wani jinjiri sabon haihuwa da aka tsinta da ransa kuma zindir a wani gona a ranar Laraba, 9 ga watan Oktoba.

An kai lamarin ne ga cibiyar Salama, asibitin Sir Patrick Ibrahim Yakowa, Kafanchan, jihar Kaduna.

Manajar cibiyar, Misis Grace Yohanna Abbin, wacce ta zanta da jaridar Daily Trust a ranar Talata, tace wata mata ce ta gano jinjirin a hanyarta na zuwa gona a Gidan Waya inda ta jiyo hayaniyar jariri a dajin.

“Sai ta ga wani jinjiri tsirara sai ta dauke shi, ta nannade shi sannan ta kawo shi cibiyarmu,” Abbin ga manema labarai kan yadda aka gano jinjirin.

KU KARANTA KUMA: Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un: Yusuf ya kashe matar shi da duka saboda kawai ta kaiwa mahaifiyarta ziyara

Wani likita da ya duba jinjirin ya gano cewa an haife sa ne kwana daya kafin yasar da shin. “Kuma yaron na cikin koshin lafya,” inji ta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel