Ko sau nawa zamu tsaya gaban alkali, mu ke da nasara, in ji ‘yan shi’a

Ko sau nawa zamu tsaya gaban alkali, mu ke da nasara, in ji ‘yan shi’a

- 'Yan kungiyar IMN wadanda aka fi sani da musulmi mabiya aqidar shi'a, sun zargi gwamnatin tarayya da kawo tsaiko akan shari'unsu

- Kungiyar ta sanar cewa, koda sau nawa zasu tsaya a gaban kotu da gwamnatin tarayya, su ne ke da nasara

- Sun zargi gwamnatin tarayyar da yiwa damokaradiyyar kasar nan karantsaye tare da take hakkin mutane

‘Yan kungiyar IMN wadanda aka fi sani da musulmi mabiya aqidar shi’a, sun zargi gwamnatin tarayya da kawo tsaiko a shari’un da suka shafi ‘yan kungiyar tasu har da ta shugaban kungiya, Sheikh Ibrahim Zakzaky.

Kungiyar ta ce, da gangan gwamnatin tarayya ke son fusata kungiyar lauyoyinsu wacce ke samun shugabancin Femi Falana, SAN da Maxwell Kyon, wadanda suka yi nasarar kare duk zarge-zargen da gwamnatin tarayyar ke musu.

KU KARANTA: Jerin sabbin dokoki 5 da shugaba Buhari yasa hannu

Kungiyar IMN din ta ce, gwamnatin tarayyar ta kawo wannan salon ne saboda bata samu nasara akan ‘yan kungiyar ba a kotu.

A takardar ranar 16 ga watan Oktoba wacce Ibrahim Musa, shugaban kungiyar yada labarai ta IMN yasa hannu, kungiyar ta ce: “A yau sati daya kenan da babbar kotun jihar Kaduna ke samun shugabancin Jastis Nyoms ta saka tare da wanke ‘yan kungiyarmu 9 wadanda aka cafke kusan shekaru 3 da suka wuce yayin tattaki zuwa makokin Ashura. An zargesu ne da laifin kawo hargitsi ga mutane kuma an gurfanar dasu gaban kuliya ne tun watan Satumba na 2016,”

“Akwai shari’u da dama da kungiyar IMN tayi nasara a jihohi da dama na kasar nan. Hakan ne kuwa ya jawo tsaikon da gwamnatin tarayya ke kirkirowa akan sauran shari’un don fusata kungiyar lauyoyinmu. Muna kira ga gwamnatin tarayya da ta janye zargin da take wa shugabanmu da sauran ‘yan kungiyarmu don ko sau nawa ne zamu maka su da kasa a kotu. Kin bin wannan shawara kuwa barazana ce ga damokaradiyyarmu da kuma rayukan ‘yan kasa.” Cewar takardar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel