Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un: Yusuf ya kashe matar shi da duka saboda kawai ta kaiwa mahaifiyarta ziyara

Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un: Yusuf ya kashe matar shi da duka saboda kawai ta kaiwa mahaifiyarta ziyara

- Wani mutumi mai suna Kazeem Yusuf ya kashe matar sa saboda kawai ta kaiwa mahaifiyar ta ziyara

- An bayyana cewa Yusuf ya sha yiwa matar ta shi gargadi akan cewa bai so ta dinga zuwa wajen mahaifiyar ta

- Zuwan da tayi na karshe shine ya bata masa rai tana dawowa ya hau ta da duka har ALlah ya karbi rayuwarta

An kama wani direban babbar mota dan shekara 28 mai suna Kazeem Yusuf da laifin kashe matar shi mai suna Raimot, saboda kawai ta kaiwa mahaifiyarta ziyara jihar Ogun.

Wannan lamari dai ya faru a cikin watan Satumbar wannan shekarar ne a gidansu dake Adatan cikin garin Abeokuta, amma kuma an kama Yusuf a ranar 14 ga watan Oktobar nan bayan ya gudu.

An bayyana cewa ma'auratan sun dan samu sabani tsakanin su, hakan ya sanya Raimot ta tafi wajen mahaifiyarta domin ta kai karar mijin nata, sai dai kuma an ce ba sau daya ba ba sau biyu ba Yusuf ya sha gargadin matar ta shi akan ziyartar mahaifiyarta da take yi.

KU KARANTA: Kano 9: Ku fita ku bar jihar Kano, Sarkin Bichi ya gargadi 'yan Kudu da suke zaune a Kano da mummunar niyya

Haka kuma, Raimot wacce take da yaro mai suna Farouk wanda ta samu tare da tsohon mijinta, tana zuwa ganin yaron nata ne wanda yake tare da mahaifiyar ta.

Wannan ziyara da Raimot ta je ta batawa Yusuf rai matuka, inda ya kirata a wayar tarho ya bayyana mata kada ta sake ta dawo masa gida, tunda ba ta jin magana.

Cikin tsautsayi sai Raimot ta dawo gida, shi kuma mijin ya hau ta da duka, suna cikin wannan rikici ne sai Allah ya dauki rayuwar Raimot.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel