Kano 9: Ku fita ku bar jihar Kano, Sarkin Bichi ya gargadi 'yan Kudu da suke zaune a Kano da mummunar niyya

Kano 9: Ku fita ku bar jihar Kano, Sarkin Bichi ya gargadi 'yan Kudu da suke zaune a Kano da mummunar niyya

- A wani taro da aka gabatar a garin Bichi tsakanin Sarkin na Bichi da kuma kwamishinan 'yan sandan jihar

- Sarkin ya gargadi dukkanin al'ummar Kudu da suke shigo jihar Kano da mummunar niyya da su tattare kayansu su bar jihar Kano

- Sarkin yayi wannan gargadi ne biyo bayan lamarin da ya faru na satar yara guda tara da aka yi a jihar Kano aka kai su Kudu aka sayar

Sarkin sabuwar Masarautar Bichi a jihar Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero ya yi Allah-wadai da yin garkuwa da yara tara ‘yan asalin Kano da waɗansu gungun masu garkuwa da mutane ‘yan ƙabilar Ibo su shida suka yi, inda suka canza musu sunaye tare da mayar da su addinin Kiristanci.

Idan ba a manta ba jaridar Legit.ng ta ruwaito muku cewa Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano ta ceto yara tara daga hannun wasu gungun ‘yan ƙabilar Ibo su shida waɗanda suka yi garkuwa da su daga Kano suka kai su jihar Anambra, suka canza musu addini zuwa Kiristanci, suka canza musu sunaye tare da siyar da su.

Sarkin ya bayar da wannan umarnin ne ranar Laraba lokacin da ya karɓi baƙuncin Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Kano, CP Ahmed Iliyasu a fadarsa dake ƙaramar hukumar Bichi.

Ya ce koda yake dai Kano birni ne mai al’adu da yawa wanda yake karɓar baƙi daga dukkan sassan ƙasar nan, al’ummar jihar ba za su lamunci waɗanda za su zo jihar da ‘mummunan niyya’ ba.

KU KARANTA: Jare Ijalana: Hotunan yarinya 'yar Najeriya da tafi kowa kyau a duniya

“‘Yan uwanmu maza da mata daga Kudancin ƙasar nan mutanen kirki ne, mummunan aiki daga ‘yan kaɗan daga cikinsu ba zai canza tunaninmu ba, amma muna buƙatar da su fito fili su yi Allah-wadai da abin gaba ɗaya," in ji shi.

Sarki Bayero ya ce waɗanda za su zo daga Kudu da ‘munanan tunani’ ya kamata su canza ko kuma su bar jihar.

Ya kuma yabi CP Iliyasu da tawagarsa ta Operation Puffe-Adder bisa ƙoƙarinsu na ceto yaran Kano guda tara daga Anambra da yadda suka mayar da su wajen iyayensu.

A nasa ɓangaren, Mista Iliyasu ya ce ya je Fadar Sarkin ne da mambobin zartawa na ‘yan kwamitin kyautata alaƙa tsakanin ‘yan sanda da al’umma, PCRC, don su gaishe da Sarkin kafin su yi taron gari da al’ummar Bichi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel