Ban ce daga Ubangiji sai Goodluck Jonatahan ba – Bala Mohammed

Ban ce daga Ubangiji sai Goodluck Jonatahan ba – Bala Mohammed

Mun ji cewa gwamnan jihar Bauchi, Dr. Bala Abdulkadir Mohammed ya fito ya yi magana a kan surutun da ake yi a gari na cewa ya ce ‘Daga Ubangiji, sai kuma shugaba Goodluck Jonathan.’

A jiya Laraba 16 ga Oktoba, 2019, mai girma gwamnan ya wanke kansa ta bakin kwamishinansa na yada labarai, Ladan Salihu. Kwamishinan yace an dauki maganar gwamnan ne daga sama.

Ladan Salihu ya ke cewa ‘yan jarida sun juya kalaman gwamnan ba yadda yake nufi ba. Salihu yake cewa abin da gwamnan ya yi, shi ne yabawa Jonathan a matsayin Maigidansa a siyasa.

Gwamnan yake cewa ya yabawa Gwaninsa watau tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ne kurum ba komai ba, inda ya kuma yi kira ga masu yada sharri su daina siyasantar da lamarin.

KU KARANTA: Wanene sabon Gwamnan Bauchi Bala Mohammed na PDP

Kwamishinan yada labaran na jihar Bauchi yake cewa ko yaushe gwamna Bala Mohammed zai yi jawabi ya kan fara ne da kiran sunan Ubangiji Allah madaukaki da kuma Annabi Muhammadu.

A cewar Ladan Salihu, gwamna Sanata Bala Mohammed ya san girman addininsa kuma ya na ganin darajarsa. Tuni dai jawabin da gwamnan ya yi kwanaki ya karade shafukan yada zumunta.

Gwamnan na jihar Bauchi ya yi magana ne a Hedikwatar jam’iyyar PDP da ke babban birnin tarayya Abuja inda ya jinjinawa Goodluck Jonathan wanda ya ba shi kujerar Ministan Abuja.

Jiya kun ji cewa Kwamishinan Bauchi ya yi murabus saboda sauya masa Ma’aikata. Nura Manu Soro ya sanar da murabus din sa ne bayan an yi rairaya a Jihar don haka ya ajiye aikinsa.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel