To fah: Ina gina masallatai ne da kudin da nake samu wajen garkuwa da mutane - In ji Lawal mai garkuwa da mutane

To fah: Ina gina masallatai ne da kudin da nake samu wajen garkuwa da mutane - In ji Lawal mai garkuwa da mutane

- Wani fitaccen mai garkuwa da mutane da aka kama a jihar Oyo ya bayyana dalla-dalla yadda yake gabatar da ayyukansa

- Ya bayyana cewa kudin da yake samu yana gina coci da masallaci ne, kuma yana daukar nauyin danginsu

- Haka kuma ya bayyana cewa iyayen shi sun san da cewa yana yin wannan sana'ar ta garkuwa da mutane

Rundunar hukumar 'yan sandan jihar Oyo ta kama wani wanda take zargin dan garkuwa da mutane ne mai suna Taofeek Lawal a garin Ibadan babban birnin jihar Oyo.

A yadda jaridar Aminiya ta ruwaito, Lawal ya bayyana cewa ya shiga sana'ar garkuwa da mutane ne don karbar kudin fansa domin ya dinga samun kudin da zai ke biyawa matar shi kudin makarantar da take yi a garin Ile-Ife dake jihar Osun.

Mutumin wanda ya bayyana cewa mutanen da yake kamawa yara ne wadanda basu wuce shekaru hudu zuwa shida ba, ya ce yana karbar naira dubu dari (N100,000) ne akan kowanne yaro guda daya da ya sata.

"Na gina gidaje guda biyu, na gina Masallaci da Coci. Ni nake daukar nauyin dangin mu, kuma iyaye na sun san irin sana'ar da nake yi," in ji shi.

KU KARANTA: Ashsha: Budurwa ta gama shiri tsaf domin aurar wani jirgin sama da ta shafe shekara biyar tana so

Haka kuma mutumin ya bayyana cewa kungiyarsu suna yiwa 'yan siyasa da kuma sarakunan gargajiya aiki a duk lokacin da bukatar hakan ta taso.

Ya kara da cewa ya so ya daina wannan halayya tashi ta garkuwa da mutane, amma wani mai sarautar gargajiya dake garin Osogbo ya kara masa karfin guiwa akan ya cigaba da yi.

Ya bayyana cewa an kama shi har sau biyar a jihar Legas, amma wannan mai sarautar gargajiyar na garin Osogbo shi ne yake zuwa ya fito da shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel