EFCC: Jami’in JAMB ya sace Naira Miliyan 20 ya zuba kwalaye - Shaida

EFCC: Jami’in JAMB ya sace Naira Miliyan 20 ya zuba kwalaye - Shaida

Wata mai bada shaida a gaban kotu a shari’ar da ake yi da jami’an hukumar jarrabawar JAMB ta Najeriya, ta bada labarin yadda Aliyu Yakubu ya yi awon gaba da makudan kudi na hukumar.

Karimatu Abubakar ta fadawa Alkali mai shari’a a babban kotun tarayya, Peter Affen cewa Aliyu Yakubu ya sace Naira miliyan 20 da hukumar jarrabawar ta tara, sannan ya kalawa wani sharri.

Abubakar ta dauke labarin komai ta fadawa Alkalin babban kotun tarayyar da ke zama a birni tarayya, Abuja. Shaidar tace bayan Yakubu ya yi wannan aiki, sai ya cika wajen ajiyar da tarkace.

Hajiya Abubakar tace Jami’in wanda shi ne shugaban hukumar na sashen Kano ya maye gurbin kudin da ya dauka ne da wasu kwalaye inda yace wani ma’aikacin banki ne ya sace miliyoyin.

KU KARANTA: Shugaban Majalisa ya shiga matsala kan zargin handame ayyukan FIRS

Shaidar da hukumar EFCC ta gabatar a karar, ta ce a 2016 ne aka bata umarni ta sakon wayar tarho daga Hedikwata ta tashi ta duk binciki katin jarrabawar da JAMB ta saida a Garin Kano.

Ma’aikaciyar wanda EFCC ta yi amfani da ita a matsayin shaida a kotu tace sai bayan da ta koma Abuja ne ta fahimci cewa tarkace ne kurum a cikin tarin kwalayen katin jarrabawar da aka ba ta.

Kamar yadda shaidar ta fada da bakin ta a kotu, ta dauki kayan ne a cikin jakar nan wanda ake kira ‘Ghana-must-go’. Wanda ake tuhuma da laifin, ya daura zargin ne a kan ma’aikatan bankinsa.

Yakubu yace jami’an banki ne su ka yaudaresa, su ka ki maido masa katin da ba a saida ba, sannan ba su ba shi kudin cinikin da aka yi ba. Mai shari’a Affen ya dage kara sai Fubrairun 2020.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel