Katin ‘Dan kasa: Akwai zalunci a matakin da Gwamnatin APC ta dauka – PDP

Katin ‘Dan kasa: Akwai zalunci a matakin da Gwamnatin APC ta dauka – PDP

Babbar jam’iyyar hamayya a Najeriya ta PDP, ta fito ta na mai kokawa da matakin gwamnatin APC ta shugaban kasa Muhammadu Buhari na karbar kudin mutane a kan katin ‘dan kasa.

Kamar yadda Sakataren yada labarai na jam’iyyar na kasa, Kola Ologbondiyan ya bayyana, yace PDP ba ta goyon bayan a rika tatsar kudi a hannun jama’a da sunan za a yi masu katin shaida.

Ologbondiyan yace: “Maganar biyan kudi domin karbar katin shaidar ‘dan kasa da gwamnatin Buhari ta kawo ba abin ba goyon baya bane, zalunci da kuma raina tunanin mutanen Najeriya.”

A cewar Kola Ologbondiyan, sake daura nauyin wani kudi a kan ‘Yan Najeriya ba ya nufin komai sai mugunta tare da karbe hakkin da kasa ta ba ‘ya ‘yan ta. Wannan ya sa PDP tace da fa sake.

KU KARANTA: Ba mu kai amince da karin albashi manyan Ma'aikata ba – Minista

A jawabin na Ogbondiyan ya ce: “Raba katin zama ‘Dan kasa hakkin ‘Yan kasa ne a kan gwamnati don haka dole a cigaba da raba wannan kati kyauta kamar yadda gwamnatin PDP ta rika yi.”

Kakakin jam’iyyar adawar a madadin PDP ya kara da yin kira ga gwamnatin tarayya ta shugaba Buhari ta yi maza ta janye maganar biyan kudi N5000 kafin ‘a jefa kasar cikin rashin sukuni.’

Mista Ologbondiyan yake cewa: “Tun kafin a je ko ina, wannan shiri ya fara jawo dar-dar inda jama’a su ke fitowa a fili, su na nuna rashin amincewarsu da wannan sabon tsari da aka kawo."

PDP ta ce kwanan nan ne gwamatin APC ta shugaba Buhari ta kara VAT zuwa 7.5%, bayan kuma karin farashin wuta da yunkurin kafa shinge da ake yi a manyan hanyoyin gwamnatin tarayya.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel