Shugaban majalisar dattawa ya samu guraben aiki 26 a hukumar FIRS

Shugaban majalisar dattawa ya samu guraben aiki 26 a hukumar FIRS

Rahoton jaridar Daily Trust ya bayyana cewa hukumar tattara haraji ta kasa, FIRS ta baiwa shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan guraben aiki guda 26 domin ya rabar dasu ga jama’an mazabarsa.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wannan bayani ya fito ne sakamakon rikicin dake neman kaurewa tsakanin Sanatocin Najeriya da hukumar FIRS game da tsarin da ta bi wajen rabon guraben ayyukan a garesu, wanda hakan yasa suke yi ma hukumar barazana.

KU KARANTA: Yan bangan siyasa sun tayar da yamutsi a yayin taron shugaban INEC da jam’iyyu

Majiyarmu ta kara da cewa tuni hukumar ta mika takardar daukan aiki ga mutanen da shugaban majalisar ya zaba don samun wannan gwaggwaban aiki, kamar yadda wani Sanata ya tabbatar.

Sanatan da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa: “Muna zargin Sanata Ahmad Lawan da kwashe dukkanin guraben ayyukan guda 26 da FIRS ta bashi ba tare da ya yi la’akari da sauran Sanatocin da suka fito daga jaharsa ba.”

Haka zalika wata kungiyar matasa dake mazabar Sanata Lawan mai suna Unity for Collective Progress Forum ta tabbatar da cewa duk wadanda Sanatan ya zaba sun samu takardar daukan aiki, kuma zasu fara aiki nan bada jimawa ba.

Kungiyar ta bayyana rabe raben ayyukan a tsakanin kananan hukumomin dake mazabar Sanatan kamar haka: Nguru 5, Karasuwa 3, Machina 4, Bade 7, Yusufari 4 yayin da Jankusko ta samu gurabe 3.

Wannan batu dai ya tayar da kura, inda wata kungiya mai zaman kanta Socia-Economic Right and Accountability ta nemi Sanatan ya tsatstsage mata bayani game da zargin da ake yin a cewa hukumomin gwamnatin tarayya sun baiwa shuwagabannin majalisar guda 10 guraben ayyuka 100.

Sai dai duk kokarin da aka yi na jin ta bakin mai magana da yawun Sanatan, da kuma mai magana da yawun hukumar FIRS ya ci tura, amma shugaban kwamitin majalisar dattawa dake kula da rabe raben ayyuka, Sanata Dajuma La’ah ya bayyana cewa sun fara gudanar da bincike a kan batun.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel