Ku dage da addu’a don shawo kan matsalolin Najeriya - Ahmad Lawan ga yan Najeriya

Ku dage da addu’a don shawo kan matsalolin Najeriya - Ahmad Lawan ga yan Najeriya

Shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Ahmad Lawan ya bayyana cewa kasar Najeriya na bukatar addu’o’I domin shawo kan dimbin matsalolin da suka yi mata katutu, musamman a wannan lokaci da ake ciki.

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito hadimin Sanata Ahmad Lawan a kan harkokin watsa labaru, Ola Awoniyi ne ya bayyana cewa sanatan ya bayyana haka ne a ranar Laraba, 16 ga watan Oktoba yayin da kungiyar yan majalisa kiristoci suka kai masa ziyara a ofishinsa.

KU KARANTA: Yan bangan siyasa sun tayar da yamutsi a yayin taron shugaban INEC da jam’iyyu

A cewar Ahmad: “Duba da halin da muke ciki a yanzu, da kuma tarin kalubalen da muke fuskanta a matsayinmu da kasa da kuma al’umman Najeriya, akwai bukatar mu dage wajen addu’a. a yau an wayi gari muna fama da matsalar tsaro.

“Inda kuma muke da jami’an tsaro wanda aikinsu ne su kare rayukanmu da dukiyoyinmu, dole ne sai mun tayasu da addu’a domin su samu daman yin aikinsu yadda ya kamata, ba wai maganan basu makamai bane kawai, ikon Allah yafi karfin duk wani makami.

“Ina fata dukkanin mabiya addinai daban daban a Najeriya zasu cigaba da taya hukumomin tsaronmu da addu’a domin su samu daman karemu.” Inji shi.

Daga karshe Lawan yace a matsayinsu na shuwagabanni zasu cigaba da gudanar da shugabanci na adalci, tare da neman shiriyar ubangiji a kan yadda suke tafiyar da shugabancin.

Shi ma a nasa jawabin, shugaban kungiyar, Sanata Emmanuel Bwacha ya bayyana cewa suna shirya taron addu’o’I ne kamar yadda suka saba duk shekara domin yi ma kasa addu’a.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel