Majalisa ta na binciken manyan motocin da Ambode ya saya na Biliyan 45

Majalisa ta na binciken manyan motocin da Ambode ya saya na Biliyan 45

Ku na da labari Majalisar dokokin jihar Legas ta na cigava da bin diddikin gwamnatin baya ta Akinwunmi Ambode. Yanzu an kai ga bin yadda aka kashe kudi wajen sayen wasu motocin haya.

Tsohon kwamishinan tsare-tsaren tattalin arziki da kasafin kudin jihar Legas, Olusegun Banjo, ya bayyana cewa Mai gidansa Ambode bai bi ta ofishinsa ba kafin ya saye dogayen motoci 820.

Akinwumi Ambode ya kashe kusan Naira biliyan 45 wajen wannan kwangila ne ba tare da ilmin Olusegun Banjo wanda ya rike ma’aikatar kasafin jihar, kamar yadda ya shaidawa ‘yan majalisa.

A Ranar Talata 15 ga Oktoba ne tsohon Kwamishinan ya hallara gaban majalisar dokokin Legas inda ya yi karin haske a gaban kwamitin mutane-16 da Fatai Mojeed ya ke binciken badakalar.

KU KARANTA: APC Jam'iyyar makartyata ce inji wani Gwamnan PDP

Mista Olusegun Banjo ya zargi tsohon Mai gidansa da sabawa dokoki inda ya fadawa kwamitin: “Yadda aka tsara ma’aikatu (a lokacin Ambode) bai ba mu damar yin aiki yadda ya kamata ba.”

“Naira bilyan 24 ba su zo ma’aikata ta ba. Ba mu da tsarin da yake aiki. A matsayin Kwamishina, ba zan iya sa hannu a fitar da Naira daya ba. Ma’aikatu kai tsaye su ke zuwa su ga gwamna.”

“Gwamnatin Ambode ba ta yi abubuwa ba ke-ke-da-ke-ke ba. Abubuwa kan faru ba da sanin Kwamishinoni ba. Ba mu san inda ake kai rarar kudi ba. Babu wanda ya fada mana.” Inji Banjo.

Akinyemi Ashade wanda ya rike Kwamishinan kudi da kuma tsohon Kwamishinan ayyuka na musamman na gwamnatin Ambode watau Oladejo Seye ba su amsa goron gayyatar majalisar ba.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel