Maganar amincewa da karin albashin 20% da 13.5% karya ne – Keyamo

Maganar amincewa da karin albashin 20% da 13.5% karya ne – Keyamo

Gwamnatin Najeriya ta musanya rade-radin da ya soma karade shafukan sada zumunta cewa an cin ma yarjejeniyar yi wa manyan ma’aikata da ke rukuni na 7014 da kuma 15-17 karin albashi.

Rade-radin da ke yawo shi ne manyan ma’aikatan kasar za su samu karin kashi 20% da kuma 13.5% na abin da su ke samu a albashinsu. Karamin Ministan kwadago ya karyata wannan batu.

Karamin Ministan kwadagon Najeriya, Festus Keyamo ya bayyana cewa har zuwa tsakiyar dare babu wata matsaya da su iya ci tsakaninsu da Jagororin kwadagon da ke wakiltar Ma’aikatan.

“Ku yi watsi da labarin da ke yawo a ko ina na cewa gwamnatin tarayya ta amince da bukatun ‘Yan kwadago na karin albashin 20% da 13.5% ga ma’aikatan da ke rukuni na 7-14 da na 15-17.”

Ministan ya fitar da hotunan zaman na su da kungiyoyin kwadago wanda ya kai har karfe 2:00 na dare inda yace babu gaskiya a maganar da ta shiga bakin jama’a na cewa an kai ga yarjejeniya.

Keyamo ya fito shafinsa na Tuwita ne a cikin daren yau 17 ga Watan Oktoba, 2019 yana cewa har zuwa cikin daren nan bangarorin gwamnati da kwadago su na kokarin cigaba da tattaunawa ne.

KU KARANTA: Akwai yiwuwar a zaftarewa masu rike da mukamai albashi

“Kamar dai jiya, har yanzu mu na cikin taro ne da ‘yan kwadago kawo yanzu cikin dare, domin mu samu maslaha game da yadda za a kasa tsarin sabon albashin ma’aikata.” Inji karamin Ministan.

Daga baya kuma Ministan ya kara fitowa ya ce: “Yanzu karfe 12:00 na dare ya wuce, mun tafi gajeren hutu saboda ‘yan kwadago su samu damar tattaunawa kan tayin da mu ka yi masu.”

Kamar yadda hotuna su ka nuna, Ministan ya na cewa: “Sun bar teburorinsu zuwa wani daki na dabam domin su yi shawara da juna.” Keyamo ya fadi wannan ne da kimanin karfe 12:19 na dare.

A daidai karfe 2:09am ya sake sanar da halin da ake ciki inda ya ke cewa: “2:00 ya wuce kuma duka bangarorin (Kwadago da gwamnati) sun amince su daga zama zuwa karfe 7:00 na yamma”

Ana sa rai cewa a Yau Alhamis, kamar lokacin da aka shirya da yamma, Ministoci da sauran Wakilan gwamnati da na Ma’aikata za su sake zama domin karkare duk abubuwan da su ka rage.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel