Bidiyo: Aisha Buhari ta nemi afuwa

Bidiyo: Aisha Buhari ta nemi afuwa

First Lady, Aisha Buhari ta nemi afuwar 'ya'yan ta, iyalanta da sauran 'yan Najeriya masu mata fatan alheri kan fitowar bidiyon da aka jiyo ta tana fada da ya karade kafafen sada zumunta.

Ta nemi afuwar ne yayin wata ziyarar goyon baya da matan gwamnonin jihohin Najeriya suka kai mata a fadar shugaban kasa a Abuja.

Leadership ta ruwaito cewa Aisha ta bukaci matan gwamnonin jihohin kada su bari bidiyon ya dauke musu hankali a cewar sanarwar da hadiminta kan kafafen watsa labaranta Suleiman Haruna ya fitar.

A makon da ya gabata ne bidiyon wata mace tana daga murya a a cikin gida cikin bacin rai ya karade kafafen sada zumunta.

DUBA WANNAN: Jigawa: Shugaban makarantar sakandare ya rasa aikinsa saboda satar kwamfuta

A lokacin da bidiyon ya fito ba a tabbatar ko wanene matar ba domin fuskanta bai fito ba.

Amma bayan ta dawo Najeriya a ranar Lahadi 13 ga watan Oktoban 2019 daga kasar Ingila inda ta shafe watanni biyu, Aisha Buhari ta ce ita ce ke cikin bidiyon.

A hirar da tayi da BBC Hausa, tayi cikaken bayanin abinda ya faru a lokacin.

Ta ce kuma Fatima Mamman Daura ce ta nadi faifan bidiyon.

Aisha ta ce, "Ni ne a ke tsaye a cikin bidiyon kuma akwai masu tsaro na a baya na.

"Fatima, 'yar Mamman Daura ce ta nadi bidiyon a gaban mai tsaro na da kowa da ke wurin. Tana nadin bidiyon ne a gaba na tana min dariya.

"Sunyi hakan ne saboda mai gida ne ya kore su a gidan. Ya ce su kwashe kayansu su barwa 'da na Yusuf gidan ya zauna.

"Na kyalle su zan koma daya daga cikin dakunnan amma suka hana ni wucewa, na kyalle su domin in bi wata hanyar amma na ga an rufe dakin ajiyan kaya (store)."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel