Sunaye da mukami: Buhari ya nadawa Aisha sabbin hadimai shida

Sunaye da mukami: Buhari ya nadawa Aisha sabbin hadimai shida

Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da nadin sabbin hadimai na First Lady ta Najeriya, Aisha Buhari kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Sanarwar da Direktan watsa labarai na First Lady, Sulaiman Haruna ya fitar ya ce wadanda aka nada sun hada da:

1. Dakta Mairo Almakura - Mai taimakawa ta musamman kan African First Ladies Mission (AFLPM)

2. Muhammad Albishir - Mai taimakawa na musamman kan Kungiyar Cigaba da First Ladies na kasashen Afirka (OAFLD).

3. Wole Aboderin - Mai taimakawa na musamman kan kungiyoyin masu zaman kansu (NGOs)

4. Barrista Aliyu Abdullahi - Mai taimakawa ta musamman kan Kafafen watsa labarai

5. Zainab Kazeem - Mai taimakawa ta musamman kan Harkokin cikin gida da taruka.

6. Funke Adesiyan - Mai taimakawa ta kusa Harkoki cikin gida da taruka

Dukkan wadanda aka nada za su fara aiki nan take.

DUBA WANNAN: Tirkashi: An tsinto wasu iyali da suka kebe tsawon shekaru 9 suna jiran 'karshen duniya'

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel