Kogi2019: jam'iyyun siyasa 45 a jihar sun bayyana goyon bayansu ga gwamna Yahya Bello

Kogi2019: jam'iyyun siyasa 45 a jihar sun bayyana goyon bayansu ga gwamna Yahya Bello

Ana saura wata daya zaben gwamnan jihar Kogi, jam'iyyun siyasa 45 a jihar sun bayyana goyon bayansu ga gwamna Yahya Bello, saboda namijin kokarin da yake yi a jihar.

Bello na neman takaran wa'adi na biyu matsayin gwamnan jihar Kogi karkashin jam'iyyar All Progressives Congress (APC).

Gamayyar jam'iyyun siyasa (CPP) a Kogi ya bayyanawa manema labarai a Lokoja, birnin jihar cewa sun marawa gwamnan goyon bayansu ne saboda ayyukan kwaran da yayi a shekaru hudu da suka gabata.

Shugabangamayyar, Dakta Sani Teidi, ya ce dukkan jam'iyyun sun natsu sun duba dukkan yan takaran zaben gwamnan jihar na bana kuma sun glura cewa babu wanda ya cancanci kujerar kamar Yahaya Bello.

Ya ce gwamnatin Yahaya Bello ta inganta abubuwa da yawa a jihar na cigaba. Hakazalika gwamnatin ta kawar da siyasar kabilanci, addini da hali.

KU KARANTA: Ku bude mana boda tun da bamu rufe namu - Kasar Ghana ta bukaci Najeriya

CPP ta yi kira ga gwamnan ya dau wannan goyon baya da suka nuna masa matsayin kira ga aiki domin cigaban jihar Kogi.

Jam'iyyun da wannan gamayya ta kunsa sune: KOWA, DA, APA, LP, NNPP, YES PARTY, AGAP, MMN, ABP, AA, SNG, NPC, NAC, BNPP, DPP, ABDP, PDC da CAP.

Sun hada da AP, AD, GPN, PPN,NCP, YDP, JMPP, ZLP, PPP, HDP, AAC da PRP.

Sauran sune: NPM, ACPN, UPP, ACD, NEPP, NDLP, NRM, AGA, DPC, NUP, RBNP, RAP, CNP, PDM and NDCP.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel