FG ta kori mambobin jam'iyyar DPRK 7, ta haramta musu dawowa Najeriya har abada

FG ta kori mambobin jam'iyyar DPRK 7, ta haramta musu dawowa Najeriya har abada

Gwamnatin tarayya ta kori wasu mambobin jam'iyyar 'Democratic People's Republic of Korea Nationals' daga Najeriya.

Shugaban hukumar hana shige da fice ta kasa (NIS), Muhammad Babandede, shine wanda ya kaddamar da umarnin mayar da 'yan siyasar kasar su ta haihuwa, Koriya, a ranar Talata.

An mayar da mutanen 7 kasarsu ne saboda sun kawo raini ga batun tsaron kasa, lamarin da yasa aka haramta musu sake dawowa Najeriya har abada.

Mutanen da aka kora sune; Jo Sun Phil, Jang Sung Chol, Che Chunk Hyok, Pak Yong Gon, Ri Yong Il, Ri Hak Su da Ri Tong Nam.

Da yake magana a kan lamarin ranar Laraba, kakakin hukumar NIS, DCI Sunday James, ya ce an fitar da mutanen bakwai zuwa kasar Koriya daga filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja.

"An fitar da su ne bisa umarnin ministan harkokin cikin gida kamar yadda dokar bakin haure ta shekarar 2015 ta bashi iko," a cewarsa.

Source: Legit

Mailfire view pixel