Ashsha: Budurwa ta gama shiri tsaf domin aurar wani jirgin sama da ta shafe shekara biyar tana so

Ashsha: Budurwa ta gama shiri tsaf domin aurar wani jirgin sama da ta shafe shekara biyar tana so

- Wata budurwa ta bar mutane cikin rudani bayan ta bayyana irin soyayyar da take yiwa jirgin sama

- Ta bayyana cewa ta gama shiri tsaf ta auri jirgin saman bayan ta yi soyayya da shi na tsawon shekara biyar

- A cewar masana matar tana fama da wata rashi lafiya mai taba kwakwalwa mai suna 'Objectophilia' a turance

Wata budurwa mai shekara 30 ta bayyana cewa tana soyayya da wani jirgin sama kuma ta gama shiri tsaf domin aurar shi. Budurwar ta bayyana cewa ta shafe shekaru biyar tana soyayya da jirgin saman.

Matar mai suna Michele Kobke wacce take a birnin Berlin na kasar Jamus, ta bayyana cewa tana soyayya da jirgin Boeing 737-800, wanda yake na daukar fasinja, har ma ta kira jirgin da sunan abin kaunarta.

Da take magana da jaridar Sun ta kasar Birtaniya, budurwar ta ce taji jirgin ya kwanta mata a rai ne. Sai dai kuma Michele ta bayyana cewa yin soyayya da jirgin sama akwai wahala wasu lokutan.

KU KARANTA: Dan gidan ministan noma yayi hadin abincin naira 30 domin tabbatar da maganar mahaifinsa

"Ina son na auri masoyin raina na zauna dashi har abada, hakan wata soyayya ce da bata cutar da kowa."

Ta bayyana cewa ta fara jin soyayyar jirgin ne a lokacin da ta hau a shekarar 2013. Ta kara da cewa jirgin yana da duk wani abu da take bukata, kuma yana saka ta farin ciki.

A cewar masana a fannin kimiyya, Michele na fama da wata cuta mai taba kwakwalwa wacce suka kirata da suna 'Objectophilia' a turance, wata irin cuta ce da mutum zai ji ya fada soyayyar wani abu wanda baya lumfashi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel