Yanzu-yanzu: Rundunar soji ta sauya sunan atisayen da ta ke yi a yankin Kudu maso gabas

Yanzu-yanzu: Rundunar soji ta sauya sunan atisayen da ta ke yi a yankin Kudu maso gabas

Rundunar Sojin Najeriya a ranar Laraba ta ce ta canja sunan daya daga cikin atisayen da ta ke yi don samar da tsaro a cikin kasar daga 'Operation Phython Dance ko Egwu Eke' a Kudu maso Gabashin Najeriya zuwa 'Atilogwu Udo'.

Mai magana da yawun rundunar sojin, Kwanel Aminu Iliyasu ne bayar da sanarwar inda ya ce sabuwar sunan ba zai canja ayyukan da masu atisayen ke gudanarwa ba na yaki da masu garkuwa da mutane, fashi da makami, da rikicin 'yan kungiyoyin asiri da sauransu.

Iliyasu ya ce, "Mahukunta a rundunar sojin Najeriya sun canja zunan daya daga cikin atisayensa mai suna 'Egwu Eke' zuwa 'Atilogwu Udo.'

DUBA WANNAN: Tirkashi: An tsinto wasu iyali da suka kebe tsawon shekaru 9 suna jiran 'karshen duniya'

An samu nasarorin sosai tun lokacin da aka kafa atisayen a 2016 zuwz yanzu.

"An kirkiri atisayen ne domin yaki da ayyukan laifuka da suka hada da garkuwa da mutane, fashi da makami, da rikicin 'yan kungiyoyin asiri da al'umma da sauran laifuka a yankin Kudu maso Gabas. Dukkan sauran ayyukan da ake gudanarwa karkashin atisayen ba za su canja ba.

"Shugaban hafsin sojojin kasa na Najeriya, Lt Janar Tukur Buratai ya sake jadada cewa rundunar sojin ta Najeriya ba za tayi kasa a gwiwa ba wurin aikinta na kare lafiya da dukiyoyin al'ummar kasar musamman a watannin karshen shekara da ake fuskantar bukukuwa."

Ma'anar Atilogwu Udo a yaran Igbo yana nufin rawan zaman lafiya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel