Dan gidan ministan noma yayi hadin abincin naira 30 domin tabbatar da maganar mahaifinsa

Dan gidan ministan noma yayi hadin abincin naira 30 domin tabbatar da maganar mahaifinsa

- Dan gidan ministan noma ya yi hadin abincin naira talatin domin tabbatar da kalaman mahaifinsa

- An nuno dan gidan ministan noman Alhaji Adamu Sabo Nanono ya sayi wake na naira ashirin da kuma nono na naira goma

- Ana tunanin dan gidan ministan yayi wannan hadi ne domin ya tabbatar da maganar mahaifinsa Alhaji Sabo Nanono

A wasu hotuna dake ta faman yawo a shafukan sadarwa na zamani, sun bayyana Alhaji Adamu Sabo Nanono, dan gidan ministan noma na Najeriya yana kwasar abinci hadin naira talatin a cikin gonar su dake kusa da garin Joda dake karamar hukumar Gabasawa a jihar Kano.

A jikin hoton an nuno ya sayi wake na naira ashirin, da kuma nono na naira goma.

Ana dai tunanin cewa Adamu ya yi wannan hadi ne domin tabbatar da kalaman da mahaifinsa Alhaji Sabo Nanono yayi, inda yake cewa kwata-kwata babu yunwa a Najeriya, har ya kara da cewa da naira talatin kacal mutum zai iya sayen abinci ya ci ya koshi ya sha ruwa a jihar Kano.

KU KARANTA: Zamu sayar da rayuwar mu domin kare hakkin Musulmai a duniya - In ji mai kamfanin Facebook

Wannan kalamai na ministan sun jawo kace-nace matuka a shafukan sadarwa, domin kuwa yayi maganar ne akan gabar da mutane ke so, domin kuwa dama kowa ta ciki na ciki ne. Hakan yasa kowa yayo caa akan shi akan wannan magana da ya fada.

Sai dai kuma mutane da yawa sun bayyana cewa wannan abinci da ya saya, koda ma ace naira talatin dinne ba zai taba kosar da shi ba, inda wasu kuma ke cewa wannan abinci yafi na naira talatin, domin kuwa a yanzu babu inda za a samu nono na naira goma.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel