Hatsarin mota ya lakume rayukan mutane 351 a jihohin arewa uku - FRSC

Hatsarin mota ya lakume rayukan mutane 351 a jihohin arewa uku - FRSC

A ranar Laraba ne hukumar kiyaye hadura ta kasa (FRSC) ta bayyana cewa mutane 351 sun rasa rayukansu, yayin da wasu 2,413 suka samu raunuka a tsakanin watan Janairu zuwa Satumba na shekarar 2019 a jihohin Benuwe, Nasarawa da Filato.

Ayobami Omiyale, kwamandan FRSC na shiyyar Filato, shine wanda ya sanar da hakan yayin gabatar da wata takardar wurin wani taro da aka gudanar a makarantar horon jami'an 'yan sanda da ke Jos.

A cewar Omiyale, hatsarin mota ya ritsa da mutane 756 a jihohin uku a cikin lokacin a tsakanin lokacin da ya ambata.

Kwamandan ya alakanta yawan afkuwar hatsarin mota da gudun wuce sa'a, amfani da waya yayin tuki, bawa yara kanana mota, fashewar taya, matsalar birki, rashin kyan hanya da sauransu.

Kazalika, ya bayyana adadin hatsarin motar ya ragu da kaso 8.3 a shekarar 2019 idan aka kwatanta da na irin wannan lokaci a shekarar 2018.

"Adadain mutanen da suka samu raunuka ya ragu da kaso 9.7, amma adadin mutanen da suka mutu ya karu da kaso 22.3," a cewar Omiyale.

Ya kara da cewa adadin mutanen da hatsari ya ritsa da su a shekarar 2019 ya ragu da kaso 7.9 idan aka kwatanta da shekarar 2018.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel