Yan bangan siyasa sun tayar da yamutsi a yayin taron shugaban INEC da jam’iyyu

Yan bangan siyasa sun tayar da yamutsi a yayin taron shugaban INEC da jam’iyyu

Wasu gungun matasa yan bangan siyasa sun tayar da rikici a yayin da shugaban hukumar zabe mai zaman kanta, INEC, Farfesa Mahmoud Yakubu ke ganawa da jam’iyyun siyasa a jahar Bayelsa inda ake tattauna shirin da hukumar ke yi gabanin zaben gwamnan jahar dake karatowa.

Jaridar The Cables ta ruwaito a dalilin haka yasa shugaban INEC, Yakubu ya fice daga wajen taron babu shiri don gudun abinda ka iya faruwa a wajen, duk kuwa da cewa an yi ta kokarin shawo kan matasan.

KU KARANTA: Ruwan sama kamar da bakin kwarya ya lalata gidaje fiye 2000, ya kashe mutum 10

Majiyar Legit.ng ta ruwaito hatta mataimakin sufetan Yansandan Najeriya daya halarci taron, sai da ya tsere daga wajen taron tare da dukkanin Yansandan da suke bayar da tsaro a wajen.

Rikicin dai ya samo asali ne bayan wani dan siyasa mai suna Francis Dakpola ya bayyana cewa an tilasta ma wasu mutane mazauna kauyen Perembiri su tashi daga garinsu sakamakon rikita rikitan siyasar zaben data gabata.

Dakpolo yace har yanzu jama’an wannan kauye basu koma kauyensu ba sakamakon rashin tabbacin tsaron rayukansu da dukiyoyinsu ba, don haka yace suna tsoron sake aukuwar sabon rikici a yayin wannan zaben gwamna dake karatowa.

Wannan magana na Dakpolo bai yi ma wasu matasan dake dakin dadi ba, inda suka nemi Dakpolo ya janye maganar da yayi, saboda a cewarsu bashi da wata alaka da kauyawan da yake magana a kansu kasancewar shi ba dan yankin bane.

A haka dai aka tashi taron baran baran kowanne bangare na barazana ga juna, wannan shine taro na biyu da hukumar INEC take shiryawa da masu ruwa da tsaki domin duba hanyoyin da ya kamata a bi don gudanar da sahihin zaben gwamnan jahar Bayelsa a ranar 16 ga watan Nuwamba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel