Ruwan sama kamar da bakin kwarya ya lalata gidaje fiye 2000, ya kashe mutum 10

Ruwan sama kamar da bakin kwarya ya lalata gidaje fiye 2000, ya kashe mutum 10

Innalillahi wa inna ilaihi raji’un, ruwan sama kamar da bakin kwarya ya lalata akalla gidaje 2,714 tare da halaka mutane 10 a jahar Neja, kamar yadda daraktan hukumar bada agajin gaggawa na jahar Neja, Ibrahim Inga ya bayyana.

Rahoton kamfanin dillancin labarum Najeriya ta ruwaito Inga ya bayyana haka ne a ranar Laraba, 16 ga watan Oktoba yayin daya bayyana a gaban majalisar dokokin jahar Neja inda ya basu bayanai game da ayyukan hukumarsa a shekarar 2019.

KU KARANTA: Yan bindiga sun yi awon gaba da jami’in KASTLEA a jahar Kaduna

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Inga ya bayyana ma yan majalisun cewa mutane 21,223 ne ambaliyan ruwan ya shafa a kananan hukumomin jahar Neja guda 20, a unguwanni 123.

“Ambaliyan ya fara ne a watan Agusta na shekarar 2019 sakamakon mamakon ruwan sama daya sauka a wannan lokaci, hadi da karfin iskan da aka dinga samu a wannan lokaci, wanda hakan ya sa aka dinga samun ambaliyan ruwa a tafkunan ruwa dake jahar.

“Wannan ambaliya yayi sanadiyyar mutuwar mutane 10, tare da karya gadoji, lalata lambatu da kuma gidajen mutane da dama saboda tsananin karfin ruwan, haka zalika ambaliyan ya lalata gonakai da dama tare da tasan mutane daga gidajensu.” Inji shi.

Sai dai Inga yace hukumarsa bata iya shawo kan matsalar yadda ya kamata ba, ko kuma ta taimaka ma jama’an da ambaliyan ya shafa ba sakamakon ta karar da kasafin kudinta na naira miliyan 200 na shekarar 2019 tun kafin farin ambaliyan.

Daga karshe Inga ya nemi majalisar ta amince da bukatar da hukumarsa ta mika na neman karin kudaden ayyuka domin ta kai agaji ga mutanen da wannan ibtila’I ya shafa a jahar Neja.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel