Gwamna Aminu Masari ya nada Prince Uche Okonkwo Mai bada shawara a Jihar Katsina

Gwamna Aminu Masari ya nada Prince Uche Okonkwo Mai bada shawara a Jihar Katsina

Mun samu labari cewa gwamnan jihar Katsina, Rt. Hon. Aminu Bello Masari ya amince da nadin Mista Prince Uche Okonkwo a matsayin daya daga cikin manyan Hadimansa.

Kamar yadda rahotanni su ka zo mana, Prince Uche Okonkwo, zai zama Mai ba gwamna Aminu Masari shawara kan harkokin kiristocin da ke zaune a cikin jihar ta Katsina.

Alhakin duk wani mutumin Ibo da ke zaune a jihar Katsina da ke Arewa maso Yammacin Najeriya ya rataya a kan wuyan Mista Prince Uche Okonkwo daga yanzu a gwamnati.

A wata takarda da ta fito daga ofishin Sakataren gwamnatin jihar Katsina aka samu wannan labari inda Mai girma SSG Dr. Mustapha Muhammadu Inuwa ya sa hannu da kansa.

KU KARANTA: 'Yan Sanda sun yi wani kame a cikin Jihar Katsina

Jama’a su na ganin wannan nadin mukami a matsayin kokarin da gwamnan jihar yake yi na ganin ya jawo kowa a jika a gwamnatinsa bayan ya shiga wa’adin karshe a Katsina.

Bayan wannan nadin mukami, mai girma gwamnan ya kuma amince da nadin Aliyu Abdullahi da Sani Mansir a matsayin wadanda za su rika taimakawa wajen harkokin yada labarai.

A karshe Dr. Mustapha Inuwa ya sanar da cewa an karawa Alhaji Sabo Musa matsayi daga matakin da yake kai na SA zuwa SSA, watau babban mai ba mai girma gwamna shawara.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel