Da dumi-dumi: Buhari ya takaita tafiye-tafiyen shugabannin hukumomi zuwa kasashen waje

Da dumi-dumi: Buhari ya takaita tafiye-tafiyen shugabannin hukumomi zuwa kasashen waje

A kokarin gyara-gyare da rage yawan kashe kudi da taka-tsantsan da baitul malin gwamnatin tarayya, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rage yawan tafiya-tafiyen shugabannin ma’aikatu, sashi da hukumomin tarayya zuwa kasashen waje.

Shugaba Buhari a ranar Laraba, 16 ga watan Oktoba, ya yi umurnin takaita tafiya-tafiyen zuwa biyu a kowani zango ya shugabannin hukumomi.

Matakin ya cigaba da bayyana cewa daga yanzu ana bukatar manyan jami’an hukumomi su gabatar da jadawalin ziyararsu zuwa ga ofishin sakataren gwamnatin tarayya a farkon shekara, jaridar Vanguard ta ruwaito.

Baya ga cewar sai fadar shugaban kasa ta amince da duk wani tafiya da gwamnati ce zata dauki nauyin sa da takardu, ya zama dole a rage tawagar minista da za su yi wani tafiya zuwa kasar waje zuwa hudu.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Yan sanda sun sake kai mamaya wata cibiyar horo a Katsina

Shugaban kasar ya kara da cewa duk wani tafiya da za a yi ya zama dole ya kasance wanda zai kawo cigaba sannan wanda kasar za ta amfana daga ciki.

A wani labarin kuma, Legit.ng ta rahoto cewa Sanata Ali Ndume ya caccaki naira biliyan 99.87 da aka warewa ma'aikatar tsaro a matsayin kasonta a cikin kasafin kudin 2020.

Sanatan mai wakilya Borno ta Kudu a majalisar dattawa ya yi korafin cewa adadin ya kasance kasa da kaso 1% na naira triliyan 10.33 da aka gabatar a matsayin kasafin kudin 2020.

Yace a matsayi kasa da ke cikin hali na yaki, wannan adadi da aka ware ya nuna cewa gwamnatin tarayya bata jajirce wajen kawo karshen yaki da ta'addanci ba.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel