SGF ya yi gargadi: Wasu na amfani da ofishina suna damfarar 'yan Najeriya

SGF ya yi gargadi: Wasu na amfani da ofishina suna damfarar 'yan Najeriya

Boss Mustapha, Sakataren gwamnatin tarayyar Najeriya (SGF) ya ce wasu 'yan damfara suna damfarar 'yan Najeriya da sunan ofishinsa.

A sanarwar da direktan yadda labarai na ofishin SGF, Willie Bassey ya fitar a madadin Mustapha, ya ce wasu 'yan damfara suna yaudarar al'umma suna karbar takardun karatunsu da sunan za su samar musu aiki bayan su biya wasu kudade.

Bassey ya kuma gargadu al'umma a kan wasu karerayi da ake yadawa a kan ayyukan mazabu da wai ofishin na SGF ke yi.

Sanarwar ta ce, "An janyo hankalin sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha kan ayyukan wasu boyayyun mutane da ke amfani da kafafen sada zumunta da wasu kafafen domin damfarar mutane da cewa su basu takardun karatunsu domin su sama musu aiki a ofishin sakataren gwamnatin tarayyar ko wasu ayyuka a ma'aikatan gwamnatin tarayya.

DUBA WANNAN: Tirkashi: An tsinto wasu iyali da suka kebe tsawon shekaru 9 suna jiran 'karshen duniya'

"An kuma sanar da ofishin na SGF kan wasu bayyanai da ake yadawa kan wasu ayyukan mazabu da ake gudanarwa karkashin sa.

"Gaskiyar lamari shine ofishin sakataren gwamnatin tarayya ba ta yin ayyukan mazabu kuma ba ta sanya ido a kan ayyukan.

"Kazalika, ofishin sakataren gwamnatin na tarayya ta gano cewa wasu miyagu sun buga wasikun bogi da suke ikirari ya fito da ofishin SGF da suka amfani da shi wurin yin maula daga wurin neman alfarma daga wurin manyan mutane da kamfanoni domin kansu."

Ya ce ana yin duk mai yiwuwa domin gano mutanen kuma a hukunta su.

"Ana gargadin al'umma su kaucewa fadawa hannun wadannan miyagun masu damfarar da ke yawa suna cutar mutane," inji Bassey.

"Gwamnati ta dauki muhimman matakai domin gano mutanen kuma za a hukunta duk wanda aka samu da hannu a cikin wannan aikin masha'an."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel