Wani mutum mai shekaru 63 kashe matarsa har lahira

Wani mutum mai shekaru 63 kashe matarsa har lahira

Wani manomi mai shekaru 63 ya shiga gidan yari a sakamakon kashe matarsa da yayi mai shekaru 38 wadda ta haifa masa ‘ya’ya biyar.

Manomin mai suna Oluwatubosun Dahunsi yayi amfani ne da adda ya sheke matar tasa mai suna Funmilayo Dahunsi a ranar 5 ga watan Oktoba, 2019 a karamar hukumar Owo ta jihar Ondo.

KU KARANTA:Babban bankin Najeriya ya fadi adadin kudin jabun da aka gano a shekarar da ta wuce

Sajan Suleiman Abdulateef, jami’in ‘yan sanda ne ya shigar da karar wannan mutum a kotu, inda ya nemi kotun da ta tsare shi a gidan yari kafin a kammala shari’arsa.

Dahunsi wanda ake zarginsa da aikata laifin a ranar 5 watan Oktoba da misalin karfe 6:30 na safiyar ranar, ya ki amsa laifin nasa. Inda ya ce shi bai aikata hakan ba.

Kamar yadda ‘yan sanda suka shigar da karar, inda ake tuhumar Dahunsi da yin amfani da adda domin ya sheke matarsa har lahira, a ranar 5 ga watan Oktoba. Wannan laifin ya sabawa sashe na 319(1) na kundin tsarin dokokin Criminal Code mujalladi na daya, 2006 na jihar Ondo.

Duk da cewa, Dahunsi bai da lauya ko guda wanda ke bashi kariya, amma ya ce shi babu abinda zai iya tunawa game da wannan al’amarin face abinda ya faru bayan sabaninsu da matar tasa.

Dahunsi ya ce: “Dan sabani muka samu game da kudin makarantar yaranmu. Ban ma san lokacin da na sheketa ba da adda. Sai bayan ta mutu na lura da abinda na aikata. Yanzu haka a cike nake da nadama, dan Allah ayi mani afuwa.”

Mai shari’a a kotun, Mrs Charity Adeyanju bayan ta saurari bayani a kan wannan karar ta dage ta zuwa ranar 13 ga watan Janairu, inda Dahunsi zai cigaba da zama gidan kaso.

https://www.vanguardngr.com/2019/10/man-63-remanded-in-prison-for-killing-wife-mother-of-five-in-ondo/?utm_source=dlvr.it&utm_medium=twitter

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel