Yanzu-yanzu: An shiga ganawa sirri tsakanin Kwadago da Gwamnati

Yanzu-yanzu: An shiga ganawa sirri tsakanin Kwadago da Gwamnati

Gwamnatin tarayya da kungiyoyin kwadago suna ganawar sirri yanzu nan domin karashe magana kan mafi karancin albashin N30,000 da yaki ci, yaki cinyewa. Daily Trust ta ruwaito.

Gwamnati tarayya ta shirya zaman domin kokarin ganin cewa ma'aikata basu tafi yajin aiki ba.

Daga cikin wadanda ke cikin ganawar sune ministan kwadago, Chris Ngige; sakatare janar na kungiyar TUC, Alade Lawal Bashir da shugabar ma'aikatan gwamnati, Folashade Yemi Esan.

Mun kawo muku rahoton cewa Kungiyar kwadagon Najeriya ta dakatad da yajin aikin da ta shirya tafiya domin cigaba da tattaunawa da gwamnatin tarayya kan sauye-sauyen da akayi cikin lamarin mafi karancin albashin ma'aikata.

Tattaunawar da aka yi na karshe ranar Talata, ba'a samu kammalawa ba amma ga dukkan alamu akwai cigaba kuma za'a cimma manufa.

Gabanin wannan sanarwa, Kungiyar ta alanta cewa ranar Laraba, 16 da watan Oktoba dukkan ma'aikatan Najeriya zasu tafi yajin aiki.

Kungiyar kwadago ta bukaci gwamnati ta kara albashin ma'aikatan matsayi 7 zuwa 24 a gwamnati da kashi 28%; hakazalika ma'aikatan matsayin 15 zuwa 17 da kashi 24%.

Amma gwamnati ta ce ita fa kashi 11% za ta iya karawa ma'aikatan matsayin 7 zuwa 14, sannan kashi 6.5% ga ma'aikatan matsayi 15 zuwa 17.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel