Yanzu Yanzu: Yan sanda sun sake kai mamaya wata cibiyar horo a Katsina

Yanzu Yanzu: Yan sanda sun sake kai mamaya wata cibiyar horo a Katsina

Runduna ta musamman daga ofishin Sufeto Janar na yan sanda a Abuja, Mohammed Adamu ta kai farmaki wata cibiyar horo a yankin Kofar Marusa dake jihar Katsina.

Mamayar da rundunar ta kai yana zuwa ne bayan an gudanar da wani aiki makamancin haka, kan wata cibiyar Islamiyya wanda wani dan shekara 78 mai suna Alhaji Abdullahi Bello Umar ke jagoranta, inda aka rufe cibiyar.

Rundunar ta isa cibiyar Malam Niga a Kofar Marusa cikin motoci uku kirar Hilux tare da wata karamar mota don gudanar da aikin wanda bai dauki tsawon sa’i daya ba.

An fahimci cewa an gudanar da aikin ne cikin gaggawa don gudun kada a san lamarin na gudana.

Wani jami’in rundunar wanda ya nemi a boye sunansa ya fada ma jaridar The Nation cewa sun tafi Katsina ne don gudanar da muhimmiyar aiki, bisa wani umurni da suka samu daga Abuja, bayan samun jawabai masu amfani daga makwabtan dake zaune kusa da cibiyar.

Daga karshe rundunar ta tafi da jagoran cibiyar da mataimakansa biyu.

KU KARANTA KUMA: Yan bindiga sun yi awon gaba da jami’in KASTLEA a jahar Kaduna

Kakakin rundunar yan sandan jihar, Gambo Isah, ya tabbatar da lamarin.

Ya jaddada cewa kwamishinan yan sanda, CP Sanusi Buba zai gabatar da jawabi ga kafofin yada labarai akan lamarin bayan wasu bincike.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel