A koda yaushe ina tabbatar da ganin cewa yan Najeriya na da abinci da hanyar shigar kudi don ciyar da iyalansu - Atiku

A koda yaushe ina tabbatar da ganin cewa yan Najeriya na da abinci da hanyar shigar kudi don ciyar da iyalansu - Atiku

Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya kuma dan takarar Shugaban kasa na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a zaben 2019, ya yi magana akan muhimmancin tsaron abinci.

Tsohon mataimakin shugaban kasar yace yana da matukar muhimmanci “a bunkasa samar da abinci da yawa, tsaron abinci da kuma noma don kasuwanci.

Atiku ya bayyana hakan ne ta shafinsa na Twitter @atiku, domin raya ranar abinci ta duniya na 2019 wanda kungiyar abinci da noma (FAO) ke rayawa duk shekara a ranar 16 ga watan Oktoba.

“Abu guda da na rika sosai sannan nake yi a koda yaushe shine tabbatar da yan Najeriya na da ayyukan yi da kuna hanyar shigar kudin siyan abinci domin ciyar da iyalinsu,”. Inji Atiku.

KU KARANTA KUMA: Kasafin 2020: Sanata Ndume ya yi korafi akan kudin da aka warewa sojoji

A baya mun ji cewa Ministan Noma da Raya Karkara, Sabo Nanono a ranar Litinin ya ce Najeriya tana samar da iasasun abinci da za ta iya ciyar da al'ummar ta har ma ta aike da saura zuwa kasashen da ke makwabtaka da ita.

The Punch ta ruwaito cewa Nanono ya ce koken da 'yan Najeriya ke yi na yunwa a kasar abin dariya ne inda ya ce babu yunwa a Najeriya.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel