Yanzu Yanzu: An sake kashe wani dan Najeriya a kasar Afrika ta Kudu

Yanzu Yanzu: An sake kashe wani dan Najeriya a kasar Afrika ta Kudu

Ana tsaka da neman hanyar kawo karshen kyamar bakaken fata a kasar Afrika ta Kudu, al’umman Najeriya a Afrika ta Kudu ta tabbatar da kisan daya daga cikin mambobinta mai suna Ikenna Otugo.

Sylvester Okonkwo, mukaddashin shugaban kungiyar Yan Najeriya a kasar (NUSA), a birnin Kwazulu Natal ya bayyana ma kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) a ranar Laraba, 16 ga watan Oktoba cewa an kashe marigayin ne a yankin Empangeni a ranar Talata.

Ya bayyana cewa wasu da ba a san ko suwanene ba ne suka kashe Mista Otugo mai shekara 41 dan asalin Nimo a yankin karamar hukumar Njikoka dake Anambra bisa sabani da ya shafi kasuwanci.

Mista Okonkwo ya bayyana ma NAN a wayan talho daga Empangeni cewa Mista Otugo yayi ma mazaunin yankin gyaran waya.

Ya bayyana cewa bayanan da aka gabatar ga kungiyar ya nuna cewa matar da ya yiwa gyaran waya bata gamsu da gyaran da Mista Otugo yayi ba.

Mista Okonkwo yace matar ta kawo wasu mutane wadanda ake zargin su ne suka daba mishi wuka.

KU KARANTA KUMA: Yanzun nan: Kungiyar NLC ta rufe ofishoshi da makarantu a Delta

Mukaddashin shugaban yace marigayin ya bar dansa dan shekara tara.

Shugaban NUSA Adetola Olubajo ya bayyana cewa an sanar da babban sakateriyar kasar game da lamarin.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel