Zamu sayar da rayuwar mu domin kare hakkin Musulmai a duniya - In ji mai kamfanin Facebook

Zamu sayar da rayuwar mu domin kare hakkin Musulmai a duniya - In ji mai kamfanin Facebook

- Mai kamfanin sadarwa na Facebook Mark Zuckerberg yayi alkawarin bada gudummawar shi wajen ganin ya kare hakkin Musulmai a duniya

- Ya ce tun yana yaro iyayen shi sun koya mishi tashi tsaye wajen kare duk wata barazana da zata shafi wasu a duniya

- Ya ce idan dan kai abu bai shafe ka ba ka bari kuma ya ci gaba da faruwa, watarana za ayi wanda zai zo ya shafi kowa da kowa

Mai kamfanin sadarwa na Facebook Mark Zuckerberg, ya ce kamfanin yana maraba da Musulmai, sannan kuma yana sanar da Musulmai cewa kamfanin zai yi iya yin sa domin ganin ya kare hakkin Musulmai.

Mark Zuckerberg yayi wannan bayani ne kwana biyu bayan dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Republican yayi kira da a hana dukkanin Musulmai shiga kasar Amurka.

Wannan nuna kyama ta addini da ake kokarin kakabawa mutanen kasar ta Amurka ya sanya mutane da dama tashi tsaye wajen ganin sun kare hakkin Musulmai ma zauna kasar.

"Iyaye na sun koya mini cewa dole mu tashi tsaye mu kare duk wata barazana da za a yiwa wani addini ko al'umma," in ji Mark Zuckerberg.

KU KARANTA: Wani tsohon najadu ya yiwa 'ya'yansa mata guda hudu fyade

"Idan an kai hari yau bai shafe ka ba, watarana za a kai wanda zai shafi kowa da kowa."

Duk da dai cewa Mark Zuckeberg bai saka wata doka da wallafa abubuwa makamantan haka a Facebook ba, amma Facebook ya bayyana goyon bayansa ga wannan barazana da ake yiwa al'ummar Musulmai.

Haka kuma shima mai kamfanin Google Eric Schmidt yayi kira da shugabannin gwamnati da kuma na kafafen sadarwa na fasaha da su hada karfi da karfe wajen kare hakkin al'umma.

A karshe dai Mark Zuckerberg yayi alkawarin mayar da Facebook ya zama tamkar mafaka ga al'ummar Musulmai da ake yi musu barazana a duniya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel