Wani tsohon najadu ya yiwa 'ya'yansa mata guda hudu fyade

Wani tsohon najadu ya yiwa 'ya'yansa mata guda hudu fyade

- An kama wani tsohon najadu da ya yiwa 'ya'yansa mata guda hudu rigis fyade

- An gurfanar da mutumin a gaban wata babbar kotu dake jihar Legas

- An bayyana cewa 'ya'yan nasa basa son halayyar shi, amma kuma shi sai ya dinga yi musu karyar wa'azi cewa babu abinda Allah zai yi musu dan ya kwanta da su

Wani mutum mai suna Bassey Archibong, wanda ya ke zaune a gida mai lamba 10 da ke kan titin Kunle Dipo a yankin Majidun Owutu cikin unguwar Ikorodu dake jihar Legas, ya gurfana a gaban kotu, bisa laifin yi wa ‘ya’yansa guda hudu fyade, wadanda shekarunsu bai wuce 12 ba zuwa 20.

An bayyana cewa, Archibong ya fara yi wa ‘ya’yansa fyade ne tun a shekarar 2016. An dai gurfanar da Archibong ne a gaban kotun Ikorodu ta jihar Legas, bisa tuhumar sa da laifuka guda uku, wadanda su ka hada da lalata da ‘ya’yansa da rashin mutunta doka da kuma bata rayuwar ‘ya’yansa.

Sai dai wanda a ke tuhumar ya musanta dukkan laifukan da a ke zargin sa da shi.

Lauya mai gabatar da kara, John Iberedem, ya bayyana cewa, Archibong ya na amfani da abinci wajen sa musa kayan maye, domin ya dauke hankalinsu wajen cimma burinsa na yin lalata da su. Iberedem ya kara da cewa, duk lokacin da zai yi amfani da su sai su ki yarda, inda su ke tunatar da shi cewa, Allah ya hana kuma ya yi alkawarin hukunta duk wanda ya ke aikata wannan lamari.

Lauyan ya cigaba da cewa, wannan laifi ne wanda ya ke da hukuncin a sashe na 265 (2) na dokar manyen laifuka ta jihar Legas ta shekarar 2019.

KU KARANTA: Abin mamaki: Dan damfara ya sayarwa da wani bature buhun gishiri naira miliyan 27 a matsayin buhun Lu'u-lu'u

Ya ce, “yaran su na wahala a duk lokacin da ya ke kwanciya da su. “Ya na mai bayyana musa cewa, babu komai idan mahaifi ya kwanta da 'ya'yansa a wajen Allah." Sannan ya kara bayyana wa yaran nasa cewa: "Allah ba zai hukunta duk wanda ya kwanta da 'ya'yansa ba.”

An dai karanta hukuncin kamar haka, “kai Bassey Archibong, a tsakanin shekarar 2016 zuwa 2019, a gida mai lamba 10 kan titin Kunle Dipo da ke yankin Majidun Owuta cikin garin Ikorodu ta Jihar Legas, ka yi lalata da yaranka guda hudu wadanda shekarunsu bai wuce 12 zuwa 20 ba, domin haka ka aikata laifi wanda ya ke da hukunci a sashe na 265 (2) na dokar manyen laifuka ta jihar Legas ta shekarar 2015.

“Kai Bassey Archibong, a wannan rana da lokaci sannan kuma a gundumar, ka yi lalata da diyarka mai shekara 20 ba tare da izinin ta ba, domin haka ka aikata laifi wanda ya ke da hukunci a sashe na 260 (1) na dokar manyen laifuka ta jihar Legas ta shekarar 2015.”

Alkali mai shari’a Misis F. A. Azeez, ta bayar da umurnin a cigaba da tsare wanda a ke tuhuma a gidan yari har sai an samu shawarwari daga ma’aikatar shari’a ta jihar. Sannan ta dage sauraron wannan kara har sai ranar 30 ga watan Oktobar shekarar 2019.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel