Shugabancin 2023: Kungiyar Ohanaeze ta caccaki Junaid Mohammed da Ango Abdullahi

Shugabancin 2023: Kungiyar Ohanaeze ta caccaki Junaid Mohammed da Ango Abdullahi

Kungiyar Ohanaeze Ndigbo ta gargadi Dr Junaid Mohammed da farfesa Ango Abdullahi da su daina amfani da lafuzai wanda ka iya janyo rashin zaman lafiya a fagen siyasa.

Kungiyar tayi magana ne ta hannun mataimakin kakakinta, Chuks Ibegbu, inda zargi mutanen guda biyu da kokarin ingiza rashin daidaituwa da kawo rabuwar kai a tsakanin jama'a.

Ha ila yau kungiyar ta kuma bukaci gwamnatin tarayya da ta gargade su aka wannan yunkui nasu.

Mataimakin kakakin kungiya ta Ohanaeze, ya yi jayayya da kuma karyata furucin Farfesa Abdullahi na cewa yankin Arewa tana dauke da mafi yawan al’umma.

Ya dage cewa rahoton Confab 2014 da kuma sake tsarin Najeriya zai amfani yankin Arewa fiye da yankin Kudu amman “mutanen nan suna cigaba da yaudarar al’umman yankin Arewa”.

Haka zalika ya bayyana farin cikinsa kan cewa yankin arewa ta tsakiya ta daina yarda da irin wannan yaudaran sannan cewa hatta ga maza da mata ya asalin arewa ma sun dawo daga rakiyar mayaudaran.

KU KARANTA KUMA: Ku hada kai da yan ta’adda ni kuma na tsige ku – Gwamnan Bauchi ya gargadi sarakuna

Kungiyar ta kara da cewa mutanen yankin sun waye kuma baza su yarda mutane irin su Junaid Mohammed da Ango Abdullahi su kara yaudaransu ba.

Ya bukaci Junaid Mohammed da farfesa Ango Abdullahi dasu tuba su kuma zama abin kwatance ga matasan yankin Arewa maimakon ingiza rashin jituwa, kasancewar su masu martaba kuma dattijai.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel