Ana daf da zaben Kogi, Yahaya Bello yayi nadin sabon mukami

Ana daf da zaben Kogi, Yahaya Bello yayi nadin sabon mukami

Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya nada Abdulkareem Jamiu a matsayin shugaban ma’aikatansa. Sakatariyar gwamnatin jihar Kogi, Mrs Folashade Ayoade-Arike ce ta fitar da wannan labarin.

Gwamnan Bello ya aminta da nadin Abdulkareem Jami’u ne a matsayin shugaban ma’aikatansa bayan da Edward Onoja yayi murabus daga kan mukamin na shugaban ma’aikatan gwamnan.

KU KARANTA:El-Rufai ya gabatar da kasafin kudin 2020 ga Majalisar jihar Kaduna

Folashade ta ce, Jami’u kafin a ba shi wannan mukamin shi ne Daraktan tsare-tsare na gwamnan jihar Kogi. Haka kuma ta kara da cewa, Dr Gabriel Ottah shi ne zai maye gurbin Abdulkareem a matsayin Daraktan tsare-tsare na gwamnan.

Haka kuma zancen na ta ya kara da cewa, wannan nade-naden sun soma aiki ne tun ranar Litinin 14 ga watan Oktoba, 2019.

Majiyar Daily Trust ta ruwaito mana cewa Edward Onoja ya yi murabus ne domin ya samu damar fuskantar takarar sa a matsayin mataimakin Gwamna Yahaya Bello a zaben gwamnan jihar da za ayi a ranar 16 ga watan gobe.

A wani labarin kuwa zaku ji cewa, Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya gabatar da kasafin kudin shekarar 2020 ga majalisar dokokin jihar ranar Talata 15 ga watan Oktoba, 2019.

Mataimakiyar gwamnan jihar Kaduna, Dr Hadiza Balarabe ce ta wakilci gwamnan inda ta gabatar da biliyan N257 a matsayin kasafin kudin shekarar 2020 ga majalisar dokokin Kaduna.

https://www.dailytrust.com.ng/kogi-governor-names-new-chief-of-staff-as-onoja-resigns.html

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel