Yanzun nan: Kungiyar NLC ta rufe ofishoshi da makarantu a Delta

Yanzun nan: Kungiyar NLC ta rufe ofishoshi da makarantu a Delta

Biyo bayan rgazawar gwamnatin tarayya wajen cika bukatun kungiyar kwadago, kungiyar Nigerian Labour Congress (NLC) a ranar Laraba, 16 ga watan Oktoba, ta fara rufe ofishoshin gwamnati da makarantu a Delta.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ta ruwaito cewa an gano mambobin kungiyar NLC a Asaba, babbar birnin jihar suna kora dalibai daga makarantun gwamnati gida

Hakan na zuwa ne yan kwanaki bayan kungiyar tayi wa gwamnatin tarayya barazanar cewa za ta fara daukar mataki idan har ba a yi wani muhimmin abu game da bukatar kungiyoyin kwadago ba.

Ku tuna cewa Legit.ng ta rahoto a baya cewa NLC ta bukaci a sanya ranar Laraba 16 ga watan Oktoba, a matsayin wani rana na ganawa tsakanin majalisar wakilai da kungiar yan kasuwa ta TUC.

Hakan ya kasance sakamakon kin halartan zaman ranar Talata, 15 ga watan Oktoba da mambobin kungiyar TUC suka ki yi.

KU KARANTA KUMA: Ku hada kai da yan ta’adda ni kuma na tsige ku – Gwamnan Bauchi ya gargadi sarakuna

A baya Legit.ng ta rahoto cewa kungiyar kwadagon Najeriya ta dakatad da yajin aikin da ta shirya tafiya domin cigaba da tattaunawa da gwamnatin tarayya kan sauye-sauyen da akayi cikin lamarin mafi karancin albashin ma'aikata.

Tattaunawar da aka yi na karshe ranar Talata, ba'a samu kammalawa ba amma ga dukkan alamu akwai cigaba kuma za'a cimma manufa.

Gabanin wannan sanarwa, Kungiyar ta alanta cewa ranar Laraba, 16 da watan Oktoba dukkan ma'aikatan Najeriya zasu tafi yajin aiki.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel