Gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana lokacin da dokar ilimi kyauta kuma dole zata fara aiki a jihar

Gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana lokacin da dokar ilimi kyauta kuma dole zata fara aiki a jihar

- Gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana cewa, nan da shekarar 2020 za a fara wajabta ilimi kuma kyauta ga kowanne fdan jihar har zuwa matakin sakandire

- Mukaddashin gwamnan jihar, Hadiza Balarabe ta sanar da hakan yayin mika kasafin kudi na shekarar 2020 ga majalisar jihar

- A kasafin kudin, fannin ilimi, lafiya da ababen more rayuwa ne suka kwashe kusan kashi 73

Gwamnatin jihar Kaduna a ranar Talata ta bayyana cewa, zata tabbatar da dokar ilimi kyauta kuma dole ga kowanne dan jihar har zuwa kammala sakandire.

Mukaddashin gwamnan jihar, Hadiza Balarabe ce ta bayyana yayin mika kasafin kudin shekarar 2020 ga majalisar jihar.

“Daga 2020, kowanne da a jihar Kaduna zai samu karatun shekaru 12 na dole kuma kyauta a jihar,” in ji ta.

KU KARANTA: Me yayi zafi? Ta kona mazaunan masu aikinta da dutsen guga

Kamar yadda kasafin kudin ya bayyana, naira biliyan 140 wanda ya fi kasha 73 zai tafi ne ga harkar ilimi, lafiya da ababen more rayuwa.

Fannin ilimi zai lashe naira biliyan 44.9, fannin lafiya zai lashe naira biliyan 30.29 sai ababen more rayuwa zasu kwashe naira biliyan 64.9.

“Mun yi niyyar mika wasu dokoki da majalisar zata duba don su kawo cigaba ga shugabancin jihar,” in ji ta.

Kamar yadda tace, dokokin zasu hada da dokar kudi; wacce zata kawo gyar ga dokar haraji da sauransu.

“A sakamakon karfafa shugabancin da muke yi a karo na biyu, zamu tabbatar da cewa mun sa bukatun mutanen jihar a farko. Zamu cigaba da ba talakawa damar bayyana bukatarsu, karfafa damammaki da kuma jawo masu zuba hannayen jari. Lokacoin kalilan ne, don haka bazamu bar wani abu ya dauke mana hankali ba.” In ji mukaddashin gwamnan jihar Kaduna.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel