An kona motoci 9 makare da Kifi da akayi yiwo safarasu daga kasar Nijar

An kona motoci 9 makare da Kifi da akayi yiwo safarasu daga kasar Nijar

Hukumar sojin Najeriya dake Damaturu sun kona motoci tara da ke dauke da gasassun kifi na miliyoyin naira da akayi kokarin shiga dasu daga kasashen waje.

An gudanar da bikin kona motocin ne a ranar Talata, a barikin sojin dake titin Potiskum, Damaturun jihar Yobe.

Kafin fara konasu, kwamandan sakta 2 na rundunar Operation Lafiya DOLE, Brig.-Gen Ibrahim Sallau ya ce rundunar 159 bataliya dake Geidam suka damke kifayen a ranar 4 ga Oktoba a Bukarti, karamar hukumar Yunusari.

Ya laburta cewa masu fasa kwabrin sun taho daga Diffa, kasar Nijar ta hanyar Hadejia ta Jigawa kafin aka damkesu a Bukarti.

SHIN KA SAMU LABARIN CEWA EFCC ta sake gurfanar da lauyan Atiku

Ya jaddada cewa na haramta kasuwancin kifi a jihohin dake yaki saboda ya ta'addan na amfani da kasuwancin wajen daukan nauyin ayyukansu.

Yace: " Masu fsa kwabrin sun shigo da haramtaccen kayen ne daga Diffa a kasar Nijar ta hanyar Hadejia a jigawa.

"An shirya kifayen cikin bawon masara cike da motocin 9. Za mu cigaba da kona dukkan kayayyakin da aka haramta a fagen yakin Operation Lafiya dole."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel