Kasafin 2020: Sanata Ndume ya yi korafi akan kudin da aka warewa sojoji

Kasafin 2020: Sanata Ndume ya yi korafi akan kudin da aka warewa sojoji

Sanata Ali Ndume ya caccaki naira biliyan 99.87 da aka warewa ma'aikatar tsaro a matsayin kasonta a cikin kasafin kudin 2020.

Sanatan mai wakilya Borno ta Kudu a majalisar dattawa ya yi korafin cewa adadin ya kasance kasa da kaso 1% na naira triliyan 10.33 da aka gabatar a matsayin kasafin kudin 2020.

Yace a matsayi kasa da ke cikin hali na yaki, wannan adadi da aka ware ya nuna cewa gwamnatin tarayya bata jajirce wajen kawo karshen yaki da ta'addanci ba.

Ndume wanda ya kasance shugaban kwamitin majalisa dattawa akan lamarin sojoji, ya ce rundunar sojin Najeriya ta cananci fiye da kudin da aka ware mata a cikin kasafin 2020.

Ya bayyana cewa rundunar soji na bukatar samun kudade domin inganta kayayyakinta don yaki da ta'addanci.

KU KARANTA KUMA: Na yi amfani da kudin fansar da na karba wajen ilimantar da matata da gina masallaci da coci – Mai garkuwa da mutane

A halin da ake ciki, Legit.ng ta rahoto a baya cewa Sanata Ali Ndume ya bayyana cewa akwai wasu kungiyoyi masu zaman kansu dake fakewa da aikin bayar da tallafi ga wadanda rikicin Boko Haram ya shafa a jahar Borno, amma suna taimaka ma kungiyar ta’addanci ta Boko Haram.

Sanatan ya bayyana haka ne yayin da yake ganawa da manema labarai a majalisar dattawa a ranar Talata, 15 ga watan Oktoba, a matsayinsa na shugaban kwamitin majalisar dake kula da rundunar Sojan kasa.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel