Ku hada kai da yan ta’adda ni kuma na tsige ku – Gwamnan Bauchi ya gargadi sarakuna

Ku hada kai da yan ta’adda ni kuma na tsige ku – Gwamnan Bauchi ya gargadi sarakuna

- Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed ya nuna damuwa akan lamarin rashin tsaro a jihar

- Gwamnan ya kuma nuna kula game da yiwuwar hadin baki tsakanin yan ta'adda da sarakunan gargajiya

- Ya gargadi sarakuna a jihar da su guji hada kai da yan ta'adda ko kuma ya tsige su

Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi a ranar Talata, 15 ga watan Oktoba, yace zai tsige duk wani basarake a jihar da aka samu da hada kai da yan ta'adda.

Gwamnan ya yi gargadin ne yayinda ya karbi bakuncin mambobin majalisar sarakunan jihar Bauchi karkashin jagoancin Sarkin Bauchi, Alhaji Rilawanu Sulaiman Adamu.

Ya yi korafin cewa yan fashi da makami da masu garkuwa da mutane da aka fatattaka daga sauran jihohi na shigwa Bauchi domin haddasa rashin zaman lafiya.

Gwamnan ya cigaba da kalubalantar sarakuna akan adalci da daidaito wajen gudanar da ayyukansu.

Ya ce gwamnatinsa za ta yi aiuki tare da hukumomin gargajiya da sauran hukumomi masu amfani domin tabbatar da cewar ayyukan ta'addanci ya zama tarihi a jihar.

KU KARANTA KUMA: Na yi amfani da kudin fansar da na karba wajen ilimantar da matata da gina masallaci da coci – Mai garkuwa da mutane

A wani lamarin kuma, Legit.ng ta rahoto a baya cewa Yan bindiga a ranar Talata, 15 ga wata Oktoba, sun kai mamaya garin Malum, wani yanki na karamar hukumar Ardo-Kola da ke jihar Taraba sannan suka yi garkuwa da Reverend Solomon Jediel.

Yan bindigan bayan sun yi gaba da mai wa’azin sun kira iyalinsa sannan suka sanar dasu cewa su fara tara kudi domin biyan fansar sa.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel