EFCC ta sake gurfanar da lauyan Atiku

EFCC ta sake gurfanar da lauyan Atiku

A ranar Talata, hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa wato EFCC ta sake gurfanar da lauyan Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar Peoples Democratic Party, Uyiekpen Osagie-Giwa.

An gurfanar da lauyan, Uyiekpen Osagie-Giwa, ne tare da 'dansa Erhunse Giwa-Osagie gaban babbar kotun tarayya dake jihar Legas an zargin almundahanar $2 million.

An fara gurfanar da su ne gaban Alkali Nicholas Oweibi a ranar 14 ga Agusta kuma sun musanta zargin da ake musu.

A wani labarin mai alaka da hakan, hukumar EFCC ta kara gurfananar da Abdullahi Babalele, sirikin tsohon mataimakin shugaban kasa ne, Alhaji Atiku Abubakar a ranar Talatan da ya gabata akan almundahanar kudade.

KARANTA WANNAN: Mafi karancin albasi: Kungiyar kwadago ta dakatad da yajin aiki, za'a cigaba da tattaunawa yau

Hukumar EFCC tana zargin Babalele ne da almundahanar $140,000 a zaben shugabancin kasa da ya gabata.

An fara gurfanar da wanda ake karar ne a ranar 14 ga watan Agusta lokacin hutun kotun a gaban mai shari'a Nicholas Oweibo.

Ya musanta laifin da ake tuhumarsa da shi kuma an bada belinsa akan naira miliyan ashirin bayan da ya cika sharuddan belin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel