Mafi karancin albasi: Kungiyar kwadago ta fasa tafiya da yajin aiki, za'a cigaba da tattaunawa yau

Mafi karancin albasi: Kungiyar kwadago ta fasa tafiya da yajin aiki, za'a cigaba da tattaunawa yau

Kungiyar kwadagon Najeriya ta dakatad da yajin aikin da ta shirya tafiya domin cigaba da tattaunawa da gwamnatin tarayya kan sauye-sauyen da akayi cikin lamarin mafi karancin albashin ma'aikata.

Tattaunawar da aka yi na karshe ranar Talata, ba'a samu kammalawa ba amma ga dukkan alamu akwai cigaba kuma za'a cimma manufa.

Gabanin wannan sanarwa, Kungiyar ta alanta cewa ranar Laraba, 16 da watan Oktoba dukkan ma'aikatan Najeriya zasu tafi yajin aiki.

SHIN KA SAN CEWA EFCC ta sake gurfanar da lauyan Atiku

Kungiyar kwadago ta bukaci gwamnati ta kara albashin ma'aikatan matsayi 7 zuwa 24 a gwamnati da kashi 28%; hakazalika ma'aikatan matsayin 15 zuwa 17 da kashi 24%.

Amma gwamnati ta ce ita fa kashi 11% za ta iya karawa ma'aikatan matsayin 7 zuwa 14, sannan kashi 6.5% ga ma'aikatan matsayi 15 zuwa 17.

Ministan kwadago, Chrs Ngige, ya bayyanawa manema labarai bayan ganawar cewa yan kungiyar kwadago su yi la'akari da tattalin arzikin kasa cikin bukatarsu.

Yace: "Ni mai sulhu ne saboda haka bani goyon bayan kowa. Kamar yadda kuka gani babu fada kuma babu wanda ya yi fushi. Wannan na nuna cewa abubuwa na gudana yadda ya kamata. Zamu cigaba gobe domin tattauna abubuwan da bamu iya tattaunawa ba."

Mataimakin shugaban kungiyar NLC, Amaechi Asugwuni, ya ce ganawar da za'ayi ranar Laraba ne na karshe.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel