Na yi amfani da kudin fansar da na karba wajen ilimantar da matata da gina masallaci da coci – Mai garkuwa da mutane

Na yi amfani da kudin fansar da na karba wajen ilimantar da matata da gina masallaci da coci – Mai garkuwa da mutane

Mambobin kungiyar da Otunba Gani Adams ke jagoranta mai suna Oodua People’s Congress (OPC), a ranar Talata, 15 ga watan Oktoba, sun kama wani mai garkuwa da mutane a Ibadan, babban birnin jihar Oyo.

Mai garkuwa da mutanen wanda ya bayyana sunan shi a matsayin Taofeek Lawal, yace shi dan asalin Osogbo ne, babban Birnin jihar Osun. Lawal ya amshi bakin cewa yana sana’ar garkuwa da mutane domin daukar nauyin karatun matarsa a jami'a dake Ile-Ife, jihar Osun.

Mai laifin wanda ya bayyana cewa mafi yawancin wadanda yake kai ma hari yara ne yan shekaru hudu zuwa shida, yace kudin fansan kowane yaro N100,000.

A cewar shi yayi nasaraR sace yara uku a Osogbo sannan uku a Legas, ya kuma siyar da dan shi don kulawa da iyalansa.

Lawal yace tawagarsa na mutane 15 ta kasance tana yi ma yan siyasa da shuwagabannin gargajiya aiki a jihar Osun a duk lokacin da suka bukaci taimakon su.

Ya kuma bayyana cewa: "Na gina gidaje biyu, wani masallaci da kuma coci. Ina kuma daukar dawainiyar iyalina daga abunda nake aikatawa kuma iyayena sun san abunda nake aikatawa."

Mai laifin har ila yau ya cigaba da bayyana cewa yana da niyyar barin wannan sana’a na garkuwa da mutane amma basaraken da ya ambata a Osogbo ne ya karfafa mai gwiwa kan ya cigaba da sana’ar. Yace an kama shi sau biyar a Legas da Osogbo, amman cewa basaraken a Osogbo ne ke karbo belinsa.

KU KARANTA KUMA: Da kaina na yi ta son a yanke kafata domin na huta – Sani Moda

Wani jami’in OPC a yankin Olaifa, Mista Babatunde Atiba ya bayyana cewa kungiyar ta sami bayanai akan harkokin dan ta'addan ta hannun wata mata.

A halin yanzu an mika Lawal ga hukumar NSCDC don bincike da fuskantan hukunci.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel