Yan bindiga sun yi awon gaba da jami’in KASTLEA a jahar Kaduna

Yan bindiga sun yi awon gaba da jami’in KASTLEA a jahar Kaduna

Wasu gungun yan bindiga sun yi awon gaba da jami’in hukumar kula da ababen hawa na jahar Kaduna, KASTLEA, mai suna PMA II Hamza a kan hanyar Birnin Gwari bayan sun kashe mutane biyu daga ciki har da jariri.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito yan bindigan sun cika hannu da Hamza ne a daidai lokacin da suka tare wasu motocin haya guda 2, inda suka bude musu wuta, wanda a dalilin haka suka kashe jariri dake hannun babarsa da wani mutumi guda, suka kuma jikkata mutane biyu.

KU KARANTA: Direbobin bankaura: Hukumar FRSC ta kama yan Achaba 728 a jahar Kaduna

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Hamza na kan hanyarsa ta komawa gidansa ne zuwa ga iyalansa a garin Birnin Gwari a ranar Juma’ar data gabata a lokacin da lamarin ya auku, kuma tun nan ba’a samu labarin inda ya shiga ba.

Wani jami’in kato da gora ya bayyana cewa: “Yan bindiga sun kai ma wasu motocin haya guda biyu hari a ranar Juma’a a kayen Gaban Gayan, gab da kauyen Kurega a kan babbar hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari, yan bindigan sun kashe mutane biyu; jariri, da wani direban mota daya, sai mutane biyu da suka jikkata kuma suna samun kulawa a asibiti, tuni dai an binne yaron kamar yadda musulunci ya tanadar.”

Da majiyarmu ta tuntubi kaakakin rundunar Yansandan jahar Kaduna DSP Yakubu Sabo game da batun, sai yace bashi da masaniya game da lamarin, sakamakon baya gari, kuma a ranar litinin ya dawo bakin aiki.

Sai dai ya yi alkawarin bincikawa ya ji, amma har lokacin tattara wannan rahoto bai bayar da wani bayani ba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel