Gwamnatin tarayya da kasar Ghana sun tattauna kan rufe iyakokin Najeriya

Gwamnatin tarayya da kasar Ghana sun tattauna kan rufe iyakokin Najeriya

Ministan harkokin kasashen ketare na Najeriya, Geoffery Onyeama da kuma takwararsa ta kasar Ghana, Mrs Shirley Botchwey, sun hau teburin sulhu kan illar da rufe iyakokin kasar nan zai haifar ga harkokinsu na kasuwanci.

Kasashen biyu sun amince da wasu sabbin tsare-tsare kan yadda za'a magance matsalolin da rufe iyakokin kan tudu na Najeriya zai zai haifar a harkokin kasuwancinsu.

Ministocin biyu sun bayyana hakan ne yayin ganawa da manema labarai a ranar Laraba bayan tattaunawar sirri da suka gudanar a tsakaninsu da juna.

Mrs Botchwey wadda ta hauro kasar nan tare da ministan harkokin kasuwancin kasar Ghana, Honarabul Alan Kyerematen, za kuma su gana da ministan kasuwancin kasar nan, Okechukwu Enelemah da kuma kwanturola janar na hukumar hana fasa kwauri, Kanal Hameed Ali.

A cewar ministan harkokin wajen Najeriya, ganawar su ta tabo illar da rufe iyakokin kan tudu na Najeriya zai haifar a harkokin kasuwancin kasashen biyu, lamarin da ya ce nan ba da jimawa ba za'a a shawo kansu.

KARANTA KUMA: Kotu ta zartar da hukuncin rataya kan wanda ya kashe ma'aikaciyar kamfanin MTN

A baya-bayan nan ne hukumar da ke yaki da fasa-kwauri a Najeriya ta ce za a ci gaba rufe kan iyokokin kasar da ke tudu har zuwa lokacin da Najeriya za ta samu cikakken hadin kai daga sauran kasashen da take makwabtaka da su.

Hukumar Kwastam ta ce harkokin tsaro da na tattalin arziki sun fara inganta a Najeriya sakamakon rufe iyakokin kasar da ke kan tudu.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel