Kotu ta zartar da hukuncin rataya kan wanda ya kashe ma'aikaciyar kamfanin MTN

Kotu ta zartar da hukuncin rataya kan wanda ya kashe ma'aikaciyar kamfanin MTN

Wata babbar kotu a jihar Kwara da ke Arewacin Najeriya, ta zartar wa wani matashi, Ogundele David, hukucin kisa ta hanyar rataya biiyo bayan laifin da ya aikata na kashe wata ma'aikaciyar kamfanin sadarwa na MTN, Abiola Tosin Ashinwo.

Daily Trust ta ruwaito cewa, kotun ta zartar hukuncin ne bisa jagorancin Alkali Adebayo Yusuf Ogundele, bayan shafe fiye da tsawon shekaru uku ana gudanar da shari'a.

Kotun ta tabbatar da zargi a kan Mista David na aikata ta'addanci kan ma'aikaciyar ta MTN ta hanyar amfani da makami na wuka wanda laifin ya sabawa sashe na 229 na dokokin kasa.

Haka kuma an tattaro cewa, kotun ta zartar da hukuncin kisa ta hanyar rataya kan Mista Ashinwo da laifin kashe Tosin ta hanyar burma mata wuka, laifin da ya sabawa sashe na 221 cikin dokokin kasar.

Alkali Yusuf ya ce kotun ta zartar da wannan hukunce ne bayan da Ogundele ya gaza kare kansa a gabanta dangane da tuhumar da tuhumar da aka shimfida a kansa.

KARANTA KUMA: Arba'een: Za mu yi tattaki cikin Najeriya a ranar Asabar - IMN

Legit.ng ta fahimci cewa, kotun ta zartar da hukuncin dauri na shekaru 25 a kan Mista Ogundele sanadiyar laifin farko na ta'addanci da ya aikata. Haka zalika ta zartar da hukuncin kisa ta hanyar rataya a sanadiyar laifi na biyu da ya aikata.

A yayin tabbatar da tuhumarta, kotun ta yi amfani da shaidu hudu wanda Abdulmumini Adebimpe, jami'in dan sanda mai shigar da kara a gabanta ya gabatar da suka hadar da Sufeto Yusuf Daudu, CPL Bunmi Adegboye, Abiola Ashinwo da kuma ASP Gbadebo Adeyemi.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel