Kakakin Majalisar Kogi ya yi fice a Najeriya

Kakakin Majalisar Kogi ya yi fice a Najeriya

Kakakin majalisar dokokin jihar Kogi, Kolawole Matthew, ya zamto bajimi cikin dukkanin kakakin majalisar dokokin jihohin kasar yayin da ya lashe kyautar gwarzon dimokuradiyya ta shekarar 2019 da muka ciki.

A rahoton da jaridar Vanguard ta ruwaito, Mista Matthew ya lashe kyautar ne a matsayin mafifici ta fuskar bajinta cikin dukkanin kakakin majalisar dokokin jihohin Najeriya.

An gudanar da bikin karamcin a Otel din Transcorp Hilton da ke babban birnin Najeriya wato Abuja a ranar Larabar da ta gabata. An karrama Mista Matthew a bainar manyan mutane daga dukkanin bangarorin harkokin rayuwa, masu ruwa da tsaki, 'yan uwa da abokanan arziki.

Da yake gabatar da jawabai yayin bikin karamcin, mai daukar nauyin shirin da aka saba gudanar wa a kowace shekara, King Fajag, ya ce shirin da aka kaddamar shekaru bakwai da suka gabata na bayar da dama ta bayar da lambar yabo da kuma karrama dukkanin masu fafutikar kare martabar dimokuradiya a kasar.

Fagaj ya ce a yayin da Najeriya ta yi riko da dimokuradiyya a matsayin tsarin gwamnatin kasa, an kaddamar da shirin bayar da lambar yabo ga masu rajin ci gaba da kwararan romon dimokuradiyya a shekarar 2012, lamari da ya ce bikin na yanzu shi ne karo na bakwai a tarihi.

KARANTA KUMA: Arba'een: Za mu yi tattaki cikin Najeriya a ranar Asabar - IMN

A rahoton da jaridar Legit.ng ta ruwaito, majalisar dattawa a Najeriya ta koka matuka kan lalacewar manyan titunan gwamnatin tarayya a fadin kasar. Majalisar ta bayyana damuwar hakan ne a ranar Talata, 15 ga watan Oktoba yayin zaman da ta gudanar cikin birnin Abuja.

Shugaban majalisar dattawan, Sanata Ahmed Lawan, ya bukaci gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari da ta gaggauta shimfida dokar ta-baci akan lalacewar manyan hanyoyin kasar.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel